BAYANI GAME DA SALLAR IDI A GIDA SABODA ANNOBAR CORONA


*BAYANI GAME DA SALLAR ĪDI A GIDA SABODA ANNOBAR KORONA*
*✍ Farfesa Sheikh Ahmad Bello Dogarawa*
*Jumu’ah, Ramadān 29, 1441 (22/05/2020)*
*GABATARWA*
Bismillahir Rahmānir Rahīm. Alhamdu lillah. Wassalātu was Salāmu alā Rasūlillah, wa Ālihi wa Ashābihi wa man wālāh.
Bayan haka:
Musulmai na da ranaku biyu da suke yin īdi a cikinsu a kowace shekara: ranar daya ga watan Shawwāl bayan kammala azumin watan Ramadān – īdul fitri (karamar salla) da kuma ranar goma ga watan Zhul Hijjah – īdul adhā (babbar salla). Ranakun īdi na daga alamomi na Allah wadanda Musulmai a ko’ina cikin duniya ke yin bukukuwa da shagulgula don bayyana godiya ga Allah saboda samun nasarar kammala wata babbar ibada, da jaddada ‘yan uwantakar addini, da kuma taya juna murna da farin cikin zagayowar ranakun da Musulunci ya ba muhimmanci. Īdul fitri na biyo bayan kammala azumin watan Ramadān; shi kuma īdul Adhā na biyo bayan nasarar kammala tsayuwar Arfa da mahajjata suka yi wanda ita ce rukunin aikin Hajji mafi girma.
A wannan shekara ta 1441 bayan hijira, wato shekarar 2020 a kalandar Bature, Allah (Madaukaki) Ya kaddara ba za a yi sallar īdi na bayan kammala azumin Ramadān (karamar salla) ba a jahar Kaduna da birnin tarayya Abuja da kuma wasu jahohi na kudu masu yammacin Najeriya saboda tsoron yaduwar annobar Korona. A ranar Talata, 26/09/1441 (19/05/2020), gwamnatin jahar Kaduna ta ba da sanarwar rashin janye dokar dakatar da sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i, kuma ta bayyana cewa ba za a fita sallar īdi ba, ballantana a yi shagulgulan bikin salla karama, irin yadda aka saba. Tun bayan wannan sanarwa, mutane suka fara yin tambayoyi game da abubuwan da ya kamata su yi, a lokacin sallar īdin bayan azumi.
A cikin wannan ‘yar makāla, in shā Allah, zan yi takaitaccen bayani game da abubuwan da ya kamata kowannenmu ya yi, gwargwadon ikonsa.
*KOMAWA GA ALLAH DA CI GABA DA RIKO DA SABUBBA*
Ba shakka, halin da a ke ciki a Abuja da jahar Kaduna hali ne na damuwa da kuma rashin jin dadi saboda dakatarwar da shugabanni suka yi ga yin sallolin Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i a masallatai na tsawon lokaci a matsayin daya daga cikin manyan matakan da a ke ganin za su taimaka wajen hana yaduwar cutar Korona a cikin jama’a. Ban da damuwar da a ke ciki ta rashin gudanar da salloli a masallaci, akwai kuma kuncin rayuwa da matsatsi da rashin walwala wadanda dokar zaman gida ta haifar wa mutane da yawa. Bayan wannan, ga tashin hankalin da aka shiga na sanarwar hana fita sallar īdi irin yadda aka saba.
Kasancewar a fahimta ta, wadannan dokoki da aka sanya, da kuma matakai da a ke dauka an gina su ne a kan kokarin tunkude barna da kuma kawo maslaha ga al’umma, duk da cewa ba shi ne abin da mafi yawan mutane ke so ba, akwai bukatar kowannenmu ya natsu, ya mayar da lamari ga Allah, kuma ya bi karantarwar Musulunci wajen mu’amala da irin wannan yanayi da a ke ciki.
Daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata kowane Musulmi ya yi, akwai:
(a) Ci gaba da kankan da kai ga Allah, da tuba gare Shi, da yawaita istigfari da sadaka, da yawaita karatun Alkur’āni da salati ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da addu’o’in neman kariyar Allah daga annobar, da kuma rokon yāyewarta da daukakewarta daga al’umma gaba daya.
(b) Yarda da hukuncin da shugabanni suka yanke da kuma karbansa da zuciya daya, da kiyaye dokokin da suka sa, tare da fatan Allah Ya sa hakan ya zama alhairi ga al’umma baki daya. Ba shi daga koyarwar Musulunci zagi ko la’antar shugabanni a cikin irin wadannan mas’aloli da suka shafi makomar al’umma. Haka kuma ba shi daga koyarwar Musulunci yin tawaye ko kira zuwa ga yin bore ga umurnin shugabanni, musamman umurnin da aka gina a kan shawarwarin amintattun kwararrun masana da kuma ijtihādin kokarin tabbatar da maslaha ga al’umma, duk da cewa ana iya samun kuskure a irin wannan ijtihādi.
(c) Kwadayi da kuma kaunar samun cikakken ladan sallolin Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i da sallar īdi a wajen Allah Madaukaki duk da cewa ba a yi ba, kasancewar ba bisa ganganci ko ganin dama ne aka ki yi ba. Hadisai sun tabbatar da cewa wadanda rashin lafiya ko tafiya (balaguro) ko wasu larurori suka hana su yin ibadodin da suka sāba yi kafin wannan lokaci, ana ba su cikakken lada tamkar sun gudanar da inadodin. Bisa irin wadannan Hadisai, abin da a ke kyautata zato kuma a ke sa rai a wajen Allah (Madaukaki) shi ne a samu cikakken lada duk wadannan ibadodi da ba a samu yinsu ba yadda aka saba saboda wannan larura.
(d) Ci gaba da riko da sabubban da za su taimaka wajen ba da kāriya daga cutar, da kuma dakile yaduwarta, da iznin Allah, bisa shawarwarin da amintattun masana fannin kiwon lafiya su ke bayarwa, tare kuma da yin tawakkali ga Allah.
(e) Taimaka wa mabukata da abubuwan da za su rage masu radadin halin da a ke ciki gwargwadon iko, kuma idan an samu dama, a yi kira ga gwamnati da kungiyoyi da daidaikun mawadata su ma su taimaka gwargwadon iko.
(f) Yin tattali da kintsi da shirin yin sallar īdi a gida, shi kadai ko tare da iyalinsa, kamar yadda aka saba yin sallar.
*HUKUNCIN SALLAR ĪDI*
A wajen mafi yawan malamai, sallar īdi Sunnah ce mai karfi. Wadansu Malamai na ganin cewa mustahabbi ce, a yayin da wasu kuma suka tafi a kan wajabcinta. Salla ce da aka shar’anta ta ga Musulmi, maza da mata. Saboda muhimmancinta, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) har umurni ya bayar game da fita don gabatar da ita, shi kuma a karan kansa, ya lazimce ta tun daga shekarar da aka fara yinta har zuwa lokacin da ya bar duniya. A cikin Hadisin Ummu ‘Atiyyah (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “an umurce mu da fitar da ‘yan mata (wadanda suka balaga) da matan aure da ke cikin dakunansu (har da wadanda ke cikin jinin al’ada) zuwa sallar īdi…” [Bukhāri da Muslim suka ruwaito]. Haka kuma, Bukhāri da Muslim sun ruwaito Hadisi cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya umurci macen da ba ta da mayafin da za ta sanya don halartar sallar īdi ta karbi aro wajen wadda ke da safayar mayafi (don dai kowa da kowa ya halarci sallar).
Ana yin sallar īdi ne a filin da aka tanada na musamman, a bayan gari. Wannan shi ne asali. Haka Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa (Allah Ya yarda da su) suka yi. Amma ana iya yin sallar īdi a cikin masallaci ko a gida idan akwai larura ko tsananin bukatar haka.
*ZA A IYA YIN SALLAR ĪDI A GIDA?*
Tabbataccen hukunci a wajen fuqahā’u shi ne idan mutum bai samu sallar īdi ba tare da Liman, saboda ya makara, zai iya yin salla raka’a biyu bisa siffar da a ke gudanar da sallar īdi a wajen. Mata da yara da ba su samu zuwa sallar īdi ba, su ma ana son su yi salla raka’a biyu kamar yadda Liman da sauran jama’a suka yi. Haka kuma, wanda ke nesa da garin da a ke gudanar da sallar īdi, da wanda bai je sallar ba saboda wani uzuri karbabbe ko saboda wata larura, su ma za su yi sallarsu ta īdi a gida; su kadai ko tare da iyalansu. Imāmul Bukhāri ya kulla bābi a kan haka a cikin littafinsa “Al-Jāmi’ As-Sahih”.
Ibn Abī Shaybah da Baihakī sun ruwaito cewa Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) ya kasance a gidansa da ke wajen da a ke kira Zāwiyyah kusa da garin Basrah, bai samu zuwa sallar īdi ba, sai ya tattaro iyalansa da barorinsa, ya umurci ‘yantaccen bawansa Abdullah ibn Abi Utbah ya yi masu sallar īdi kamar yadda a ke yinta a cikin gari. Haka kuma Baihaqī ya ruwaito cewa duk lokacin da sallar īdi ta kubuce wa Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi), yana tara iyalansa su yi sallar īdi kamar yadda Liman yake yi. Bayan wannan, Abdur-Razzāq ya ruwaito cewa an tambayi Abdullah dan Mas’ūd (Allah Ya yarda da shi) game da wanda ya rasa sallar īdi, sai ya bayyana cewa zai sallace ta kamar yadda Liman ya yi.
Bayan Imāmul Bukhāri ya kawo atharin Anas dan Mālik da ya gabata, ya kuma ruwaito daga Ikramah (Allah Ya jikansa) ya ce: “Wadanda ke zaune a bayan gari za su hadu, su yi sallar īdi kamar yadda limamin cikin gari yake yi.” Atā dan Abī Rabah (Allah Ya jikansa) shi ma ya ce: “Wanda ya rasa sallar īdi (tare da Liman), zai yi raka’a biyu (kamar yadda Liman ya yi).” Ban da wannan, Baihaqī ma ya ruwaito daga Muhammad dan Sīrīn, ya ce: “Sun kasance (wato Sahabbai) suna son idan mutum ya rasa sallar īdi, ya samu fili, ya yi salla kamar yadda Liman ke yi.” Haka kuma, Abdur-Razzāq ya ruwaito kwatankwacin wannan hukuncin daga Qatādah da Ma’amar (Allah Ya jikansu), kamar yadda shi ma Ibn Abī Shaybah ya ruwaito daga Al-Hasanul Basrī da Ibrāhim An-Nakh’ī da Hammād (Allah Ya jikansu). Bayan wannan, Abdur-Razzāq da Ibn Abī Shaybah sun ruwaito cewa lokacin da ‘Amr dan Al-Aswad Al-‘Ansī da Mujāhid dan Jabr Al-Makkī suka gudu, suka būya saboda tsoron Hajjāj dan Yūsuf Ath-Thaqafī, sun rika yin sallolin īdi a wajen da suka būya.
A cikin sharhohin da suka yi wa Sahīhul Bukhārī, Ibn Rajab Al-Hanbalī da Ibn Hajar Al-Asqalānī duk sun inganta mafi yawan wadannan āthār da aka ruwaito daga Sahabbai (Allah Ya yarda da su) da Tābi’ai (Allah Ya jikansu) game da halascin yin sallar īdi a gida ga wanda uzuri ya hana shi zuwa. A cikin littafin “Al-Mughnī”, Ibn Qudāmah ya danganta irin wannan fahimtar ga Imām Mālik da Imām Ash-Shāfi’ī da Imām Abū Thaur da Imām Ibnul Munzir (Allah Ya jikansu). Haka kuma, a cikin littafin Al-Insāf, Al-Mardāwī ya danganta irin wannan fajimta ga mazhabar Imām Ahmad ibn Hanbal (Allah Ya jikansa). Sai dai kuma ‘yan mazhabar Hanābilah na da ra’ayin idan mutum zai yi sallar īdi a gida, shi kadai ko tare da iyalinsa, zai iya yin raka’a biyu ko raka’a hudu, kamar yadda Ibn Qudāmah da Al-Mardāwī suka bayyana, sannan suka rinjayar da yinta bisa siffar da Liman ke yinta saboda āthār da aka ruwaito daga Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) da Tābi’ai da yawa (Allah Ya jikansu).
Bisa bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa ya halasta a yi sallar īdi a gida saboda uzuri karbabbe ko kuma larura da za su hana a yi sallar a filin da aka saba yi, kamar yadda zai kasance a Abuja da jahar Kaduna da wasu jahohin da ke kudancin Najeriya. A kasar Saudi Arabia da Egypt da wasu kasashe da dama duk ba za a yi sallar īdi a wuraren da aka saba yi ba saboda tsoron yaduwar annobar Korona. Kwamitocin fatawa na kasashen Saudi Arabia da Egypt sun ba da fatawar halascin yin sallar īdi a gida, bisa la’akari da wasu daga cikin dalilan da na ambata a sama.
A nan Najeriya, zuwa yanzu, majalisar malamai ta jahar Kano ta nuna damuwarta game da iznin da gwamnatin jahar ta ba da a kan a fita zuwa sallar īdi duk da yawan karuwar adadin wadanda suka kāmu da cutar Korona a jahar. A mataki na kasa baki daya, Jamā’atu Nasril Islām (JNI) ita ma ta shawarci Musulmi a kan su yi sallar īdi a gida, sannan ta yi kira da babbar murya ga mutanen da ke jahohin da aka ba da damar fitowa yin sallar īdi a kan su bi dukkan tsare-tsaren da aka ce za a yi don dabbaka shawarwarin amintattun kwararrun masana. A yankin kudu maso yamma kuma, hadaddiyar kungiyar al’ummar Musulmai ta kudu maso yamma (Muslim Ummah in the South West of Nigeria – MUSWEN) da kungiyar da ke fafutukar kāre hakkokin Musulmai (Muslim Rights Concern – MURIC) duk sun fitar da sanarwar jawo hankali Musulmin da ke zaune a yankin nasu cewa su yi hakuri, su yi sallar īdi a gida, su kadai ko tare da iyalansu, ka da su je filin īdi ko da kuwa an ba su damar yin haka. Bisa wannan, duk wanda ke zaune a daya daga cikin jahohin da a ka ba da damar zuwa sallar īdi, kuma ya ga shi din bai natsu da shiga cikin daruruwa ko dubban mutanen da za su halarci sallar ba, yana da damar ya yi sallarsa ta īdi a gida.
*YADDA ZA A YI SALLAR ĪDI A GIDA*
Bayani ya gabata cewa siffar sallar īdi a gida iri daya ne da yadda a ke yinta a filin īdi tare da Liman. Huduba ce kawai ta banbanta su. A magana mafi karfi da rinjaye, idan za a yi sallar īdi a gida, ba za a yi huduba ba. Wannan shi ne abin da atharin Anas dan Mālik (Allah Ya yarda da shi) ya nuna kuma shi ne ra’ayin da Imāmul Bukhāri ya karkata gare shi.
A dunkule, ga abubuwan da ya kamata a lura da su dangane da sallar īdi:
(a) Lokacin sallar īdi na farawa ne daga lokacin da nafila ta halasta bayan fitowar rana, kamar yadda Hadisin da Abu Dāwud da Ibn Mājah suka ruwaito ya tabbatar. Lokacinta na fita da zarar rana ta wuce tsakiyar sama, wato lokacin da rana ta yi zawāli.
(b) An so a gaggauta gabatar da ita da zaran lokaci ya yi, musamman idan sallar īdin layya ne. A cikin littafin “Al-Mughnī”, Ibn Qudāmah ya bayyana cewa ba bu sabani tsakananin malamai game da bukatar gaggauta gabatar da salla a ranar layya, da zaran lokaci ya yi.
(c) An so a yi wanka kafin a yi sallar īdi [Baihaqī ya ruwaito Hadisi]; a sanya tufafi mafi kyawu [Tabarānī ya ruwaito Hadisi]; a ci wani abu, musamman dabino, kafin a yi sallar, tunda dai karamar salla ce, bisa Hadisin da Bukhāri da Tirmizi suka ruwaito.
(d) An so a yi kabbarbari tun daga lokacin da aka fara taruwa a wajen da za a yi sallar har zuwa lokacin da wanda zai jagoranci sallar zai iso wajen, bisa Hadisin da Ibn Abī Shaybah ya ruwaito. Wadansu malamai na ganin dacewar a fara yin kabbarbari tun daga lokacin da aka samu labarin tabbatar da ganin watan Shawwāl har zuwa lokacin da za a fara sallar īdi, bisa fahimtar Zaid dan Aslam da Imām Ash-Shāfi’ī (Allah Ya jikansu) game da aya ta 185 cikin suratul Baqarah, kamar yadda ya zo cikin littafin “Al-Awsat” na Ibnul Munzir.
(e) Yadda a ke yin kabbarbarin, kamar yadda Ibn Abī Shaybah da Hākim da Baihaqī suka ruwaito, shi ne mutum ya ce: “Allahu akbar, Allahu akbar, Lā ilāha illallah, Allahu akbar, Allahu akbar, wa lillahil hamd”. Haka kuma, ya tabbata cikin atharin Abdullah dan Mas’ūd (Allah Ya yarda da shi) wanda Ibn Abī Shaybah da Baihaqī suka ruwaito, mutum na iya fadin: “Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Lā ilāha illallah, wallahu akbar, Allahu akbar, wa lillahil hamd.”
Ga yadda siffar sallar īdi ta ke:
(1) Ba a kiran salla ko yin ikama a wajen sallar īdi. Hadisin ‘Abdullah dan Abbās (Allah Ya yarda da su), da Hadisin Jābir ibn ‘Abdullah (Allah Ya yarda da su) wadanda Bukhāri da Muslim suka ruwaito duk sun tabbatar da cewa ba a yin kiran salla ko ikama a wajen sallar īdi, a zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).
(2) Sallar īdi raka’a biyu ce kawai; ba a yin nafila kafin a yi sallar, kamar yadda ba a yin nafila bayanta.
(3) Ana fara sallar īdi ce da kabbarar harma tare da niyya. Daga nan sai a yi kabbarbari guda bakwai (bayan kabbarar harma) a raka’ar farko, sannan a yi kabbarbari guda biyar a raka’a ta biyu bayan kabbarar dagowa daga sujuda ta biyu ta raka’ar farko [Abu Dāwud da Ibn Mājah].
(4) An so a karanta surah al-`A’alā a raka’ar farko bayan an karanta fatiha, da surah al-Ghāshiyah a raka’a ta biyu, kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yi. Amma kuma ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana karanta surar Qāf da al-Qamar wani lokaci [Muslim da Abu Dāwud da Tirmizī]. Idan mutum bai hardace ko daya daga cikin wadannan ba, sai ya karanta surorin da suka saukaka gare shi.
(5) Bayan an kammala salla, ba wata huduba da za a gabatar. Wasu malamai na ganin ba laifi mutum ya dan fadakar da iyalinsa tare da kwadaitar da su a kan ayyulan alhairi da nisantar munanan ayyuka, ba tare da ya yi shi a siffar huduba ba.
*BIKI DA SHAGULGULAN SALLA FA?*
Ya halasta a yi wasa, da bayyanar da farin ciki, da walwala, da anashuwa a ranar īdi, matukar dai ba a ketare iyakokin da Shari’a ta gindaya ba, kuma ya zamanto yin hakan ba zai kai ga saba wa dokar zaman gida da hana cunkoson mutane a waje daya ba. Hadisai da dama da suka hada da wadanda Nasā’ī da Ibn Hibbān suka ruwaito sun tabbatar da halascin haka. Bayan wannan, mata na iya yin kida da waka a ranakun īdi (matukar ba su hada da kalmomin bātsa ko kuma cundanya tsakanin maza da mata ko su yi kida da wakar a gaban maza ba), kamar yadda Hadisin da Ahmad da Bukhāri da Muslim suka ruwaito ya nuna. Idan kuwa bai kubuta daga wadannan matsaloli ba, to ba za a yi ba.
Haka kuma, ya halasta a yi wa juna barka da salla, da addu’ar fatan alhairi, da dacewa, a ranar īdi. A cikin Fathul Bārī, Ibn Hajar ya nakalo daga Jubair ibn Nufair (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “A zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), idan mutane (daga cikin sahabbai) sun hadu da juna (a kan hanya), sukan ce wa juna: ‘Taqabbalallahu minnā wa minka’ (Allah Ya karba mana, mu da kai).”
*GYARA KAYANKA*
Lalle ne mu yi kokarin kiyaye wadannan abubuwa:
(1) Fitar da Zakātul Fitr ga duk wanda ke da iko, kafin a yi sallar īdi a ranar salla ko kuma kwana daya ko kwana biyu kafin ranar salla. Hausawa kan kira ta da suna zakkar fidda kai ko zakkar kono, kasancewarta wajibi ne da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya wajabta fitar da ita a karshen watan azumi, kamar yadda Hadisai ingantattu suka nuna. Zakkar ta wajaba a kan kowane Musulmi; yaro ko babba, mace ko namiji, mai ‘yanci ko bawa. Illa iyaka, mai gida shi ne ke fitar wa yara da mata da bayi da kuma duk wadanda ke karkashinsa, kamar yadda Hadisin da Baihaqī da Ad-Dāra Qutnī suka ruwaito ya tabbatar. Ana fitar da ita ce daga nau’o’in abincin da mutane ke ci. Adadin da a ke fitar wa kowane mutum, shi ne sā’i daya; wato mudun nabiyyi guda hudu. Sunnah ta tabbatar da cewa ana ba da zakkar ce daga nau’o’in abincin da mutane ke ci, ba daga wani abu, madadinsa ba. Hadisin da Bukhāri da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa’īd al-Khudri (Allah Ya yarda da shi) da ya yi magana a kan zakatul fitri, da lokacin da suka kasance suna fitar da ita a zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya bayyanar da haka karara. Ke nan, ba za a ba da wani abu daban, a maimakon abinci ba. Wannan ya sa mafi yawancin malamai suka ce bai halasta a fitar da kudi ko wani abu ba, a madadin abinci, domin kamar yadda suka ce, zakatul fitri nau’i ne na ibada da aka iyakancewa jinsi, don haka, dole ne a tsaya a kan nassi. Hikimar wannan zakka ta hada da tsarkake mai azumi daga kurakuren da ya yi a lokacin da ya ke azumi, da kuma samar da abinci ga miskinai, kamar yadda Hadisin da Abu Dāwud da Ibn Mājah suka ruwaito ya nuna.
(2) Ba a raya daren īdi da ibada, kasancewar ba bu wani Hadisi ingantacce da ya nuna shar’ancin hana ido barci don yin nafila da karatun Alkur’āni da zikiri a wannan dare. Hadisan da aka ruwaito dangane da falalar raya daren īdi, masu tsananin rauni ne, kamar yadda malaman Hadisi suka tabbatar. Amma mutumin da ya saba tashi cikin dare don yin ibada, zai iya yin ibadarsa a daren īdi, tunda bai kebance ibadar da wannan dare ba.
(3) A yi hattara game da nau’o’in sabon Allah da a ke yi, da sunan bayyana murna, a wannan rana, maimakon gode wa Allah bisa ni’imominSa. Kamata ya yi a gode wa Allah ta hanyar kiyaye dokokinSa, ba kuma a saba maSa ba. Abin takaici, a kan samu wanda bai taba yin zina ko shan taba sigari ko giya ba, amma a wannan rana ta farin ciki zai fara!
*KAMMALAWA*
Ina rokon Allah (Madaukaki) Ya karba mana ibadodinmu kuma Ya sa mu yi sallar īdi lafiya. Allah Ya magance mana wannan annoba ta Korona don mu samu damar komawa cikin masallatanmu, mu ci gaba da ibāda yadda muka saba.
Alhamdu lillah.
DOGARAWA (29/09/1441 - 22/05/2020)
Post a Comment (0)