SALLAR IDI DA HUKUNCINTA 2

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*SALLAR IDI DA HUKUNCINTA*_
       ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                 _*FITOWA TA BIYU*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

          ```HUKUNCIN SALLAR IDI```
            ➖➖➖ ➖➖➖➖
_Malamai Sun Tafi Akan Cewa Sallar Idi Wajibi ne. Wannan Shine Zantukan Malaman Mazhabar Hanafiyya Kuma Wannan Shine Zancen *Sheikhul Islam Ibn Taimiyya (rh)*. Sunyi Bayanin Dalilansu na Wajabta Sallar Idi da Cewa: Lallai *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Kasance Yana Sallatar Idi Bai Ta6a Fashi ba Har Yabar Duniya._

_Wasu Malaman Kuma Cewa Sukayi Sallar Idi Fard Kifaya ce (Wato Wasu Zasu Iya Daukewa Wasu). Wannan Shine Ra'ayin Mazhabar Hanãbila. Wasu kuma Sun Tafi Akan Cewa Sallar Idi Sunnah Ce Mai Karfi. Wannan Shine Ra'ayin Mazhabin Shafi'iyya da Malikiyya._

     _*HUKUNCIN AZUMI RANAR IDI*_
        ➖➖➖➖➖➖➖➖

_Haramun Ne Musulmi Yayi Azumi Ranar Idin Azumi da Idin Layya da Kuma Kwanaki Ukun Bayan Sallar Idin Layya. Malaman Musulunci Gaba Daya Sun Tafi Akan Haka Saboda Hadisin *Manzon Allah (ﷺ)* da Yake Cewa:_
عن عمر بن الخطاب رصي الله عنه قال: *”ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢَ ﻳﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺻﻮﻡِ ﻫﺬﻳﻦِ ﺍﻟﻴﻮﻣﻴﻦِ، ﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻓَﻔِﻄْﺮُﻛﻢ ﻣﻦ ﺻﻮﻣِﻜُﻢ ﻭﻋﻴﺪٌ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤﻰ ﻓَﻜُﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﺤﻮﻡِ ﻧﺴُﻜِﻜﻢ“*

_An Kar6o daga *Umar bn Khaddab (ra)* Yace: *“Naji Manzon Allah (ﷺ) Yana Hana Yin Azumi a Wadannan Ranaku Guda Biyu. Amma Ranar Idin Azumi, Itace Ranar da Zaku Bude Baki daga Azuminku. Ita Kuma Ranar Idin Layya, To Kuci daga Naman Abin Yankanku”*._

     _*LADUBBAN SALLAR IDIN AZUMI*_
    ➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
_Idin Azumi Ta Kunshi Wasu Ladubba da Hukunce-Hukunce da Suke Bukatar Dukkan Musulmi Ya Kiyayesu Domin Samun Cikakken Lada a wurin Ubangiji. Ladubban Sun Hada da:_

_*1. FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI:* Bayar da Zakkar Fidda Kai Wajibi Ne Akan Dukkan Musulmi Mai Iko. Ana Iya Bayar da Ita a Kowane Lokaci Kafin Ayi Sallar Idi. Zakkar Tana tsarkake Ran Mai Azumi ne ba Dukiyoyin Mutane ba. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_
عن أﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ، ﻗﺎﻝ: *”ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺮﺽَ ﺻﺪﻗﺔَ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻃُﻬْﺮَﺓً ﻟﻠﺼﺎﺋﻢِ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﻓﺚِ ﻭﺍﻟﻠّﻐْﻮِ ﻭﻃُﻌْﻤَﺔً ﻟﻠﻤﺴﺎﻛﻴﻦِ“*

_An Kar6o Daga *Ibn Abbas (ra)* Yace: *“Lallai Manzon Allah (ﷺ) Ya Farlanta Zakkar Fidda Kai Don tsarkake Mai Azumi Daga Alfasha da Munanan Zantuka Kuma Kuma ta Zamo Abinci Ga Miskinai”*._

_*2. KABARBARI RANAR IDI:* Sunnah Ce Yin Kabarbari Ranar Idi. Ana Farayi Ne a Safiyar Ranar Har Zuwa Idar da Sallar Idin. *Allah* Madaukaki Yana Cewa:_
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ: *”ﻭَﻟِﺘُﻜْﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟْﻌِﺪَّﺓَ ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ“*

_*“Kuma domin Ku Cika Kwanakin Kuma Ku Girmama Allah Game da Shiriyar da Yayi Muku Lallai Zakuyi Godiya”*._

_*3. CIN WANI ABU KAFIN FITA SALLAH:* Yin Hakan Riko Ne da Sunnar Annabi Mai Girma. Hadisi Ya Tabbata Cewa:_
عن ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : *”ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﻐﺪﻭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﻛﻞ ﺗﻤﺮﺍﺕ، ﻭﻳﺄﻛﻠﻬﻦ ﻭﺗﺮًﺍ“*

_An Kar6o Daga *Anas bn Malik (ra)* Yace: *“Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Baya Sammakon Fita Sallar Idin Azumi Har Sai Yaci Dabinai. Kuma Yana Cinsu ne Witri”*._
```{Bukhari}```

_*4. YIN WANKA DA CIN KWALLIYA:* Hakika *Manzon Allah (ﷺ)* da Sahabbansa Sun Kasance Suna Yin Wanka Sannan Suci kwalliya Idan Zasu Tafi Sallar Idi. Hadisi Ya Tabbata Cewa:_
عن ﻣﺎﻟﻚ ﺑﻦ ﻧﺎﻓﻊ قال: *”ﺃﻥ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻛﺎﻥ ﻳﻐﺘﺴﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﻐﺪﻭ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺼﻠﻰ}*

_An Kar6o daga *Malik bn Nãfi'u* Yace: *“Lallai Ibn Umar Ya Kasance Yana Yin Wanka Ranar Idin Azumi Gabanin Yayi Sammakon Zuwa Wurin Sallar Idin”*._

_*5. YIN SALLAR IDIN A FILI:* Hukuncin Sallar Idi Sunnah ce. Sallace da Akeyin Raka'oi Biyu Ba'ayi Mata Sunnar Sujjadar Qabliyya ko Ba'adiyya, Kuma Ba'ayi Mata Kiran Sallah Ko Iqamah._

_*6. SAUYA HANYA:* Yana Daga Cikin Ladubban Sallar Idi Sauya Hanya Yayin Dawowa. Ya Zamanto Hanyar da Akabi Yayin Zuwa Sallar daban da Hanyar da Akabi Yayin Dawowa._
عن ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ، ﻗﺎﻝ : *”ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻳﻮﻡ ﻋﻴﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺍﻟﻄﺮﻳﻖ“*

_An Kar6o daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Yace: *“Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Duk Ranar Idi Yana Sa6a Hanya”*._

_*7. BAYYANA FARIN CIKI DA ANNASHUWA:* An Kar6o Hadisi dag Uwar Muminai Tana Cewa:_
*{عن ﺃﻡ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗﺎﻟﺖ : " ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻲَّ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢ ﻭﻋِﻨﺪِﻱ ﺟﺎﺭﻳﺘﺎﻥِ، ﺗُﻐَﻨِّﻴﺎﻥِ ﺑِﻐِﻨﺎﺀِ ﺑُﻌﺎﺙَ : ﻓﺎﺿﻄﺠﻊ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔِﺮﺍﺵِ ﻭﺣﻮَّﻝ ﻭﺟﻬَﻪ، ﻭﺩﺧﻞ ﺃﺑﻮ ﺑﻜﺮٍ ﻓﺎﻧْﺘَﻬَﺮَﻧِﻲ، ﻭﻗﺎﻝ : ﻣِﺰْﻣﺎﺭﺓُ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥِ ﻋِﻨﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲِّ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢ، ﻓﺄﻗﺒﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡُ ﻓﻘﺎﻝ : ﺩﻋْﻬُﻤﺎ......}*

_An Kar6o daga *Aisha Uwar Muminai (ra)* Tana Cewa: *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Shigo a Wurina Akwai Wasu Yara Mata Guda Biyu Suna Rera Wakar Bu'as, Sai Ya Kishingida Akan Shimfida Ya Juya Fuskarsa. Sai *Abubakar* Ya Shigo Ya Fara Hantara Na Yana Cewa Sarewar Shedan a Wurin *Manzon Allah (ﷺ)!* Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Fuskanceshi Yace: *“Ka Rabu Dasu”*.........._

_*8. GAISHE-GAISHE:* Yana Daga Cikin Ladubban Ranar Idi Shine Gaishe Gaishe tsakanin Musulmai da Kuma Ziyartan Juna tare da Gabatar da 'Yan Kyaututtuka._


_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_

*سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*

_*✍🏼Sulyman Yahya*_
      _{Abu Aysha Almaliky}_

*📞+2347055883010*

*Zaku Iya Bibiyar mu a Shafin Facebook ta Wannan Adireshin👇🏽👇🏽*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

_*Ko A Telegram ta:*_

https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg


Post a Comment (0)