DANGANE DA FALALAR GOMAN ƘARSHE

Dangane da falalar goman karshe. 

Tabbas babu wasu kwanaki da dararen su ke da falala irin wadannan kwanaki da muka shiga a yau (daren 21).

Hadisi ya inganta daga Nana Aisha, kamar yadda Imamul Bukhary ya ruwaito, tana cewa:

2024 عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ : كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ شَدَّ مِئْزَرَهُ وَأَحْيَا لَيْلَهُ وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ. 

Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya Kasance idan kwanaki goma (na karshen Ramadan) suka shigo, yana tanke kwarjallen sa, yana raya daren sa kuma yana ta da iyalan sa. (Bukhary). 

A wani hadisin, cewa tayi: Annabi ya kasance yana cewa:
" تَحَرَّوْا لَيْلَةَ الْقَدْرِ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ ".
Ku nemi lailatul Qadari a goman karshen Ramadan.
Wannan hadisi na biyu sai ya nuna mana cewa yanayin duk abinda hadisi na farko ya ambata ne don neman dace da daren lailatul qadari. 

Wadannan hadisai suna shiryar damu darussa kamar haka:

1. Falalar da wadannan darare ke da shi.
2. Yadda ya kamata mu zage damtse wurin yin ibada cikin wannan darare.
3. Annabi ya kasance yana kara kaimi wurin ibada, har yana tanke kwarjallen sa (ma'ana yana nisantan iyali) don ya ba da lokacin sa sosai ga ubangijin sa.
4. Ana raya wadannan darare ne da yawan ibada, kamar salla, zikirori da sauransu.
5. Mutum zai iya ta da iyalan sa suyi ibada cikin wadannan darare tare, musamman a wannan lokaci da babu daman zuwa yin tahajjud a jam'i.
6. A wadannan kwanaki ake kirdadon lailatul qadari, wanda yafi dare dubu albarka da falala. Wanda yazo cikin wani hadisin Annabi yana cewa:
مَنْ قَامَ لَيْلَةَ الْقَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا ، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ.
Duk wanda yayi tsayuwan daren lailatul qadari yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abinda ya gabata na zunuban sa. Allah kuma da kansa Ya ce ibada cikin ta yafi yi a dare dubu da babu ita a ciki. 
7. An fi tsammanin wannan daren ciki kwanakin wutiri (21, 23, 25, 27, da kuma 29). Don haka ko da sakaci zai kama mutum, to ya kama shi a wasu kwanakin ba wadannan ba.

Allah nake roko ya datar da ni da ku baki daya. Ya sa mu samu albarka da ke cikin wannan dare, Ya bamu ikon dagewa cikin ibada, Ya kuma karba mana daidai. Allah Ya sa Muna cikin Wadanda zai you 'yanta cikin wannan wata mai alfarma.

وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين.

Post a Comment (0)