KADA KU HANASU IN SUN TAMBAYE KU


*_KADA KU HANA SU IDAN SUN TAMBAYE KU!!!_*


Dukkan Yabo ya tabbata ga Allah shi kadai.

To ya halarta mata suje masallaci suyi salla, idan sun kiyaye wasu sharuÉ—a. Amman baya cikin sharaÉ—in cewa sai muharraminsu ya rakasu, saboda haka babu komai akan su suje masallaci suyi salla ba tare da muharrami ba. 

*An faÉ—a a cikin Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah, 7/332 cewa:* Ya halarta wa mace musulma tayi salla a masallaci kuma mijinta bashi da iko ya hanata idan ta tambayi izininsa akan zata je, saboda haka matuqar dai tayi shiga ta kamala, ta rufe jikinta. An karbo daga É—an ‘Umar yace: Naji Manzon Allah (ï·º) yace: “Idan matanku suka tambayeku izini zasu je masallaci, to ku basu izini.” A wata ruwayar kuma, “Kada ku hana mata zuwa masallaci idan suka tambaye ku izini.” Bilal – É—an Abdullahi ibn Umar – yace, “Da yardan Allah, zamu hana su.” Sai Abdullahi yace dashi, “Ina ce maka Manzon Allah (ï·º) yace.…’ kai kuma kana cewa, zaka hana su?!” Duk waÉ—an nan ruwayat É—in suna cikin Muslim.

Idan mace bata tsare kanta ba, wato jikinta ya bayyana wanda haramunne wanda ba muharraminta ya gani ba, ko ta sa turare mai Æ™arfi, to anan bai halarta a gare ta ta fita ba a wannan hali, barinta fita a haka zai iya jawo fitinah. Allah yace: “Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu (daga kallon abubuwan haramun), kuma su tsare farjojinsu (daga zina) kuma kada su bayyana Æ™awarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna Æ™awarsu face ga mazansu..” [suratul Nur :31].

Da Fadinsa: “Ya kai Annabi! Ka ce wa matan aurenka da 'yã'yanka da matan muminai su kusantar da Æ™asa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauÆ™i ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai Jin Æ™ai.” [Suratul Ahzaab 59].

Zainab al-Thaqafiyyah ta kasance tana ruwaito cewa Manzon Allah (ï·º) yace: “Idan kowanne daga cikîn ku (mata) ta je sallar Isha'i, to kada ta saka turare a wannan daren.” A wata ruwayar, “Idan ko wacce daga cikin ku (mata) taje masallaci, to kada ta saka turare a wannan daren.” Duk Imamu Muslim ya ruwaito cikin Sahihinsa.

Ya tabbata cikin sahihan hadisai cewa matan sahabbai sun kasance suna zuwa sallar asuba a jam'i, suna rufe fuskarsu, ta yadda babu wanda zai gane su. Ya tabbata cewa ‘Amrah bint Abdurrahman tace: Naji Aisha, matar Annabi (ï·º), tace: “Idan Manzon Allah (ï·º) yaga yadda mata suke mu'amala, to da ya hana su zuwa masallaci kamar yadda matan banu Isra'il aka hana su.” An ce da ita ‘Amrah: Shin matan 'ya'yan banu Isra'il an hana su zuwa masallaci? Sai tace: Eh. Shi ma Imam Muslim ya ruwaito shi.

Wannan magana tana nuna mana cewa idan matan musulmi sukayi shiga wacce musulunci ya umarta suka kiyaye daga shigarsu ta yadda fitinah bazata faru ba tsakaninsu da masu raunin imani, to babu wani dalili da zai hana su zuwa masallaci suyi sallah kuwa! Idan kuma suka yi shiga ta fitsara, ta yadda da masu karfin imanin da masu raunin imani dukkansu zasu fitine su, to bai halarta ta je sallaci ba, balma baya halarta ta fita daga gidanta taje masallaci.
Wannan magana ta Nana Aisha, naji ko nace naga wani a Facebook yana kafa dalili da ita akan cewa Haramunne mata suje masallaci, bai kayyade mana ba, akan shin idan sunyi shiga ta kamala pha ya halarta ko bai halarta ba? Kawai sai yayi jam'i baki É—aya yace haramunne fitar mata zuwa masallaci tunda ga waccen maganar, to ni inaga ko raunin fahimta, ko san zuciya, ko kuma dai bai fuskanta ba ne! Allah ya shiryar damu.

*Shaykh Ibn ‘Uthaymeen ya faÉ—a cikin Majmoo’ al-Fataawa, 14/211 cewa:* Babu wani rashin dai dai akan mata suje sallar tarawee idan babu hatsarin fitina, matuqar dai sun kiyaye shigarsu kuma basu sa kayan ado ba da sauransu.


A cikin littafinsa *Hirasat al-Fadeelah (p. 86), Shaykh Bakr Abu Zayd ya lissafo wasu sharuÉ—a wa mata idan zasu je masallaci. Yace:* Tabbas ya halarta mata suje masallaci bisa wannan sharuÉ—a:

Sai dai zan kawo sharuÉ—an daga baya, fatana yanzu shine mu fahimta cewa *YA HALARTA MATA SUJE MASALLACI, KUMA DOLE IDAN SUKA TAMBAYA A KYALE SU MATUQAR SUN KIYAYE SHIGARSU!* Masu haramtawa kai tsaye, kodai raunin fahimta, ko karancin karatu, ko kuma son zuciya musamman Æ´an aqida boko. 


Allah ya tsare mana imaninmu, Kuma ALLAH NE MAFI SANI.


✍️Rubutawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey*
01/06/2019.


https://t.me/sawtul_hikmah

https://www.facebook.com/sawtulhikmah

_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙 (da'awar sunnah a social Media's) 🌎*_

*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wadannan Numbobi kamar haka:- +2348060027244 ko +2348039375380 a whatsapp.*
Post a Comment (0)