TAMBAYA 120

```Assalamu Alaikum
Mace ce ta balaga lokacin kuruciya na balaga yana damunta sai ta kasance bata yin sallah har tsawon shekara uku shin zata rama wadannan sallolin? Amma daga baya da hankali yazo mata babu sallar da ke wuce ta.```


_*AMSA:*_
*******

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،

Muna godewa Allah da ya albarkace ta da shiriya da kuma tuba daga yanayin sakaci data kasance acikinsa. Muna rokon Allah ya cika amincin sa agare ta, ya kuma bata istiqaamah akan bin dokokin sa da shiriya a hanya miqaqqiyah.

Gameda rama sallolin da batayi ba acan baya, akwai ra'ayi biyu na Malamai. Wasu Malamai suna ganin cewa wajibi sai ta rama, wannan shine ra'ayin jumhur na Malamai. 

Wasu Malamai kuma basa ganin cewa mutumin da baya sallah acan baya zai rama sallolin bayan ya tuba. Dalilin su shine a lokacin da baya sallah shi ba Musulmi bane, saboda haka idan ya tuba, toh kamar wanda ya musulunta ne, kuma shiga musulunci yana goge daukacin kurakurai da akayi kafin a shiga musuluncin.

Wasu Malamai kuma basa ganin cewa wanda ya daina yin sallah da gangan zai rama sallolin bayan ya tuba, koda shi musulmi ne ko ba musulmi ba, saboda abinda shara'ah tayi magana akansa shine wanda barci ya dauke baiyi sallah ba, ko kuma wanda yayi mantuwa baiyi sallah ba, (su kadai ne zasu rama sallah).

Daidaitaccen ra'ayi anan shine: Duk wanda yabar sallah da gangan ba tareda wani uzuri na shara'ah ba (uzurin shara'ah shine *Barci* ko *Mantuwa*), toh bazai rama sallolin ba. Amma abinda zaiyi shine ya tuba, sannan ya lazimci yawai sallar Nafilah, da fatan Allah zai yafe masa ya kuma karbi tuban sa.

Cewar wanda ya tuba sai ya rama abinda ya bari a baya na salloli ko azumi, wannan yana sanya masu wannan laifin suji wahalar tuba, sai su yanke tsammanin samun yafiyar Allah. 

Yanzu misali ita baiwar Allah idan akace sai ta rama sallolin shekara uku ai zata sha wahala sosai har ta kasa. Amma dai ana so wanda ya tuba ya yawaita aiki nagari, saboda Allah madaukakin sarki yana cewa: 

_وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ اهْتَدَىٰ._
*طـه (٨٦)*

_Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'annan kuma ya nẽmi shiryuwa._



 والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_

Post a Comment (0)