HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 2


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```// 002``` 
.
Maganar gaskiya ita ce: Tsananin son mutum ga kaiwa ga nasara ke sanya shi yan fara fafutukar kaiwa ga gaci, wanda yake son ya zama soja shi yake da lokacin kallon sojoji da ganin yadda suke fareti, wata qila ya shiga qungiyar agaji ko wata qungiya mai kayan sarki, ka ga yana son jin duk wani abu da yake da alaqa da sojojin, ya fara tambayar hanyoyin da zai bi ya shiga cikinsu, idan suka fara dauka ya je ya saka sunansa in da rabo sai dai ka ji an ce ya zama soja, ko kudi kake nema Allah SW bai zubo su daga sama kamar ruwa, duk wanda yake roqon Allah arziqi da wahala ka ji ya ce yana so ne kawai ya bude daki ya gan su a zube, hanyar isa gare su yake nema.
.
Wanda yake tsananin son abu yakan dage ne, ai mai son dan tsuntsu shi yake bin sa da jifa, ba yadda za a yi zomo ya kamu maka daga zaune, duk wanda ya ci shi ya ci gudu, akwai buqatar jajurcewa sannan a sa Allah a gaba, a nemi albarkarsa, wannan kawai ya isa komai, a wannan shiri za mu yi qoqari wurin binciko wasu hanyoyi na cin nasara da Allah SW ya shar'anta, da wasu abubuwa wadanda tabbas sun faru ga wadanda suka yi nasara a rayuwarsu, ita nasarar kalma daya ce, kuma abu guda ce, sai dai kowa da hanyar da yake bi don ganin ya kai gare ta, kuma akan yi dace din, domin na ga wani hanshaqin mai kudi da aka ce da wanki da guga ya fara.
.
Na ga wani dan kasuwa da shago sama da daya kowanne makade da kaya, ga kudi ga kyakkyawar mata, kuma aka ce ya baro gida almajirci ne a qarshe ya fada wata hanyar har ya zama haka, na hadu da wani babban malami kuma babban dan sanda, muna tattaunawa yake ce min shi daga karatun allo ne da yake sun haddace Qur'ani aka dauke shi a makarantar sakandare ta Larabci, sai ga shi har qasar waje ya fita ya dawo ya shiga aikin dan sanda ya kai wannan matsayin, na ga wani daga gini ya fara har ya mallaki gidansa na kansa ya zo ya fara yi wa wasu hanyar samun haya, har ta kai ga shi ma yana da gidaje barkatai.
.
DA FARKO ME KAKE SO?
Dole sai ka san abinda kake so sannan ka cimmasa a rayuwa, ka zama malami, likita, jami'in tsaro, lauya, babban dan kasuwa, mai sarauta ko ma'aikacin gwamnati? I to za a iya samun bambanci saboda yanayin bambancin mutane da abinda suke so, ko bambancin al'ada, da ma mataki na ilimi, sai dai a qarshe kowa za ka taras yana da abinda yake so ya cimmasa, akwai wanda za ka ga ko addu'a yake yi ba ya nufin a ba shi abinda ya roqa, ya ambaci wani abu ne amma yana nufin a ba shi abinda ba shi ya roqa ba.
.
Misali: Mun yi wani limami da kullum muka zo salla zai ya roqi Allah ya sauko mana da kabukka na ambinci kala daban-daban daga sama, tun muna yara yake addu'ar har muka girma muka san ma'anar addu'ar muka tambaye shi "Amma kai baba a yadda kake zaune haka ka ga abinci na saukowa daga sama za ka tsaya?" Ya ce ai ba abincin yake nufi ba arziqi ne, to ko arziqin ne Allah ba ya zubo kudi haka kawai, tabbas akwai arziqi kuma ba mai iya yi wa mutum sai Allah, hurumi ne daza a roqe shi, amma ba ka nade hannu Allah ya zubo maka daga sama ba.
.
Kowa ya qudurta a zuciyarsa cewa yana son ya sami kaza, ko ya zama kaza, ko ya isa zuwa wuri kaza, amma kar ya yarda ya sami abubuwa barkatai da za su cunkushe masa ya kasa tabbatar da abu guda da zai fara nema, in dai kana da abinda kake so wanda za ka fara aiki dominsa to roqi Allah sai ka fara, zan ba da misali, wata 'yar uwata ce ta kusa matuqa, maraici ya gigitata ko kuma yanayin wurin da ta taso ba wuri ne da zai taimake ta ta cika burinta na zama ma'aikaciyar jinya ba.
.
Kuma abinda take so kenan a rayuwarta, har ta ce in ba ta yi ba in sha Allah 'yarta za ta yi, ba ta da takarda sai ta Furamare, koda yake ta fara sakandare sai dai ta tuqe, haka ta yi aure, mijin da yake irin ustazannan ne ya kai ta makarantar Islamiya, ta gama ta shiga sakandare ta Islamiya, Larabci ta iya, sai aka kawo wani shiri qarqashi jama'atu na ba da taimakon farko, ai kuwa ta shiga ta yi wata shida suka yi jarabawa aka tura ta asibiti don sanin makamar aiki, jajurcewarta da iya aikin ya sa asibintin suka yarda da aikinta har suka dauke ta gwargwadon addu'arta da samun natsuwa da hukuncin Allah SW.
.
Amma mutum ya qi karatu ya nade hannu ya ce likita yake so ya zama, ko yana karatun kimiyya ne amma lauya yake so ya zama, ko ka iske wanda yake son ya zama madogara cikin manazarta a harshen Larabci amma baida littafan Larabcin, bai da daliban, a dakinsa akwai littafai sama da 500 amma duk na addini ne, kuma ya qi natsuwa ya karanci addinin, kullum shi ne a masallatai da makarantun koyar da addini da wahala ka ga ya isa inda yake so sai dai kame-kame, na san wanda tun muna sakandare yake da digirin farko ga shi na kawo inda nake a yau har yanzu bai qara ko taqi daya ba kuma yana fagen.

Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)