HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 1


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```// 01``` 
.
CIN NASARA
In aka ce nasara ana nufin isa ga biyan buqata, ko samun abinda ake nema, in mutum ya ci nasara to ya iya rinjayar qalubalen dake gabansa kenan, kalmar nasara ba ta zuwa ba tare da mutum ya tsallake wani tarnaqi dake gabansa ba, kenan maganar da Bahaushe yake cewa "Kowa ya ci zomo ya ci gudu" ta zama gaskiya, wani malamimmu Ustaz Ya'qub yake cewa ba abinda ake samunsa a bagas, in ka ga mutum ya ba ka abu ba tare da neman wani abu ba, kar ka yi zaton bagas ne ka ci baki bude, ka jira abinda zai biyo baya.
.
In ka ba Bature kyauta zai karba ya ajiye sannan ya tambaye ka "Me kake so na yi maka?" Bai yarda akwai kyauta ba dalili ba, hatta almajirai masu bara a qasashensu ba a jefa musu kudi haka arha, sai sun yi busa ko rawa da za su ja hankalin mutane, sannan a biya su, kenan samun nasara a rayuwa in muka dubi abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa yana nufin cikar burin mutum ne a kan abinda yake haqilo tuntuni, kamar mallakar gida na kai, yin tafiye-tafiye, ko samun sabbin abubuwa na more rayuwa, kodai mutum ya wayi gari kuma ga kudi a banki bai da buqatar sai ya fita kafin ya sami na rufin asiri.
.
Ko ya kasance yaransa suna karatu a manyan makarantun da ake buqata, ko kuma a ce kowa na sha'awarsa yana fatar ya zama kamarsa, ko samun wani shugabanci na gwamnati ko na al'umma, ko ya riqa ganin dandazon mutane suna zuwa wurin wata sana'a da ya fara, koda kuwa qarama ce wace ba ta taka kara ta karya ba, idan ya kalli jama'ar kuma ya ga don wannan abinda ya yi ne lallai zai san cewa ya ci nasara a ruwarsa.
.
Bai tsayanan ba, mutum ya rabu da damuwa ma wani abu ne, to bare a ce ba ya tsoron wani abinda zai bijiro masa a rayuwa, kamar a ce ma'aikacin gwamnati ne amma yana da wata sana'a a gefe da take yi masa komai, in yau ya rabu da aikin gwamnatin ba abinda zai dame shi tabbas ya yi nasara, ko in ya ga mutane na girmama shi, in ya yi magana ana sauraronsa ba don ya fi sauran 'yan unguwar ilimi ko girman shekaru ba, tabbas wannan ma zai iya zama cin nasara a rayuwarsa.
.
Babban abinda ke damun mutane a yau shi ne rashin tabbacin wurin aiki, ma'ana kullum mutum yana qoqari ne ya kawo abinda zai tabbatar da shi a inda yake samu, yana kuma tsoron kuskuren da zai yi a ce masa ya kama gabansa, to in ya sami damar kawar tsoron da yake addabarsa ya yi nasara kenan, kawar da irin wannan qalubalen bai yuwuwa sai in ba wani a samanka wanda zai ce "Kama hanya", bare kuma a ce zai iya daukar nauyin wasu mutane wadanda a qarqashinsa suke, abincinsu na samuwa ne daga wani abu da ya qirqira, kodai su dauka su je su sayar, ko kuma su taimake shi aiki, ya yanka musu albashi, wannan duk ci gaba ne ( Takbeerut Tafkeer na David p9).
.
NASARA CE ASALIN JIN DADI
Da yawanmu ba su fahimtar nasara da irin wannan bayanin da muka yi ba, domin tunaninsu kawai abinda za su ci ko su rufa asiransu su da iyalinsu, wani ma zai ce maka "In ka sami abida za ka ci ka sha ka yi zumunci ya ishe ka" ma'ana mutum bai da wani abu a rayuwa sai dai wannan, ya manta cewa maganar zumuncin da kudi ake yi, sannan zai yi tattalin abinda yake da shi a yanzu, ta yadda za a same shi a kullum, ko a qara yawansa tunda ana haihuwa iyali na qaruwa.
.
Da irin wannan ne za ka ga mutum ya rayu kullum cikin tsoron rasa abinda yake hannunsa na kudi ko na aiki ko muqami, kullum hankalinsa yana kan dan kadan din da yake hannunsa, a zahiri duk wanda ya saka a ransa cewa ba zai iya zama wani abu ba da wahala ka ga ya zama din, don ba zai taba yin abinda zai kai shi wurin ba, ko mace da take ganin ita wata ce kar ka zaci tana da abinda wata ba ta da shi ne, ta dauki kanta ne ta kai wani matsayi shi ya sa take jin tabbas tana da matsayin.
.
Mutum ya tabbatar wa kansa cewa tabbas zai iya yin kaza, shi zai sa ya fara laluben hanyoyin da zai cimma burinsa, to ko bai sami abinda yake so duka ba za ka ga ya sami wani abin, misali saurayin da yake ganin zai iya riqe mata, zai iya yin aure ka ga abokinsa da ya fi shi albashi ya cin abinci a gidansa, ga shi da qarancin albashin yana zaune da iyali, abokin kuma tsoron ciyarwa da riqe matar ya hana, ba wani abu yake hana matasa isa wurin da suke so ba sai rashin motsawa tun farko, in ka ga abokinka ya fi ka.walwala da walawa yana aikatuwar da ba ka yi ka bincika, kowa ya ci zomo ya ci gudu..

Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)