No title



*TAMBAYA*❓

shin ko ya halasta mata suyi kasuwanci a muslunci?

*AMSA*👇

Eh halatta mata su yi kasuwanci a cikin gidajensu ko kuma a waje muddin zasu kiyaye abinda shari'ah ta tanada wato kada su nuna tsiraicinsu, kada suyi tafiya ba tare da muharraminsu ba, kada su rinka nuna kwalliyarsu wato su saka hijab, kada suyi cudanya da maza, kada su rinka kashewa abokan kasuwanci maza murya yayin cinikayya, a takaice dai su kiyaye da dukkan wata kofa ta fitinah da kuma sabawa Allah da ManzonSa. Dalili kuwa shine fadar Allah subhanahu wata'ala cewa: "Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba"

‏( ﻭَﺃَﺣَﻞَّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﺒَﻴْﻊَ ﻭَﺣَﺮَّﻡَ ﺍﻟﺮِّﺑﺎ ‏)

[al-Baqarah 2:275]

Da kuma fadar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam da aka tambaye shi wane samu ne yafi? Sai yace:

( ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺑﻴﺪﻩ ، ﻭﻛﻞ ﺑﻴﻊ ﻣﺒﺮﻭﺭ ‏)

Wato samun da mutum ya nema da hannuwansa, kuma dukkan huldayyar kasuwanci (wato na halal) mai albarka ne.

Wadannan hukunce-hukuncen sun shafi dukkan musulmi maza da mata.

Haka kuma an ruwaito cewa matan Musulmi na farko suma suna kasuwanci ba tare da nuna tsiraicinsu ba, nuna kwalliyarsu ba, tare da kiyaye dukkan sauran abubuwan dake iya haifar da fitinah da sabon Allah. Amma idan mace tana kasuwanci tana bayyana kwalliyarta da yawace-yawace ba tare da muharrami ba ko kuma cudanya da mazan da ba muharramanta ba to wannan kam haramun ne..

والله أعلم،

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)