WA ZAN AURA?

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*WA ZAN AURA???*
Tambaya ce mai muhimmanci da ya kamata duk wani mai niyyar yin aure ya tambayi kan sa. 

Akwai qualities ɗin da addinin musulunci ya shar’anta ga mace ta gari da namiji na gari. Wadanda su ya kamata mu fara dubawa wajen neman aure ba wai kyale-kyale da san ran mu ba.

No hurry in life, Mu natsu wajen zaben abokan rayuwar mu, kada san zuciya ya kai mu ya baro mu, mu kyautata niyyar mu sai Allah ya taimake mu.

A duk sanda mutum zai nemi aure ya sa aranshi cewa zai yi wannan auren ne dan cika umarnin Allah madaukakin sarki da kuma ɗabbaka sunnar Annabi S.A.W, nemi zabin Allah wato istikhara sai Allah ya zamo ma jagora a cikin lamuran neman auren ka.

Da yawan matasa ba su damu da neman zabin Allah ba, burin su dai tunda su na son abu to sai sun yi.
*ISTIKHARA* tun farko ya kamata mutum ya yi ta, kafin soyayyar abu ya yi nisa cikin zuciyarka. Misali ka ga yarinyar da ka ke so, kafin ka faɗi ma ta ya kamata ka fara neman zabin Allah, haka ke ma mace kafin ki amshi tayin soyayyar shi ya kamata ki nemi zabin Allah, kada babbar mota, kuďi, katon mansion, kyau ya rude ki. Ki cire wadannan abubuwan ki sa a ranki cewa zabin Allah ki ke nema, kuma kina son yin aure ne dan neman lada wajen Ubangijinki ba dan kawarki ko yar uwarki tayi aure ba.

Wasu na aure ne dan ganin shekarunsu sun ja, gida an matsa ma su su yi aure,abokansu sunyi aure, wasu dan ba su da masoya, dan su sami mai taimakonsu ko dan wata bukata ta kansu. Mutum ya cire duk wadannan abubuwan ya sa a ran shi cewa zai yi ne dan Allah dan kuma ya cika rabin addininsa.

Da yawa iyaye da al’umma na taimakawa wajen ingiza wadanda basu yi aure ba zuwa wrong hand, saboda yawan maganganun su.
Kira na ga wadanda ba su yi aure ba su natsu kada Surutun mutane yasa su yi auren je ka nayi ka.
Toshe kunnuwanku ku natsu wajen zaben abokan zama, tunda dai ba wanda zai zauna ma ku a gidajen aurenku.

Ba wai ina nufin mata ko maza ku bijire ma iyayenku ba, a’a ku yi amfani da tausasam kalamai wajen nusar da su illar uzzurawa mutum wajen neman aure, na san ba za’a rasa wanda ka san ko ki ka san irin haka ya faru da shi ko ita.

Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)