KWANAKIN WATAN RAMADAN SUN ƘARE

KWANAKIN WATAN RAMADHAN YA KARE, AMMA HAKKOKIN ALLAH BA SU KARE WA AKANKA SAI RANAR DA YAKININ KA (MUTUWAR KA) TA RISKE KA.

ALLAH Yace'; ka bauta wa UBANGIJIN ka har sai yakini (mutuwa) tazo maka !

ALLAH shine UBANGIJIN watan RAMADHAN, da kuma watan shawwal kuma shine UBANGIJIN dukkan sauran watanni na sheka gaba-daya !

Ka zamto mai tsoron ALLAH cikin dukkanin watanni kuma ka kiyaye addinin ka cikin dukkan rayuwar ka, domin addinin ka shine kan dukkan abunda kake da shi a wurin UBANGIJIN KA tsarkakakke maɗaukaki, kuma riko da addini shine zai tseratar da kai daga wuta, don haka ka kiyaye addinin ka kayi riko da shi cikin dukkanin watanni da kuma lokuta ! 

Muna fara BIBIBIYAR watan watan RAMADHAN ne da godiya ga ALLAH, sai kuma istigfa'ri, sa'annan mu bi ta da farin ciki da falalar ALLAH da ya bamu ikon azumtan ta da kuma tsayuwar ta zuwa karewar ta ! 

Muna farin ciki da wannan ni'imar da ALLAH ya azurta mu ne,
ba wai muna farin ciki bane da karewar ta, muna farin ciki da samun daman mun gama azumtar ta da tsayuwar ta cikin ibadar ALLAH !

GARGADI MAFI GIRMA !
Mu nisanci kuma mu tsoraci yawan wasa da gafala da kuma tozarta ɗa'a ga ALLAH, domin lallai shaiɗan shi mai kwaɗayi ne da ya ɓata mana ayyukan mu, ya kuma goge mana dukkan ayyukan alkhairi da muka aikata !

Sai ya fara raya wa wasu shashin mutane daga cikin mu, idan watan RAMADHAN ya kare to lokacin takura ya kare, ya fita daga kurkuku, sai ya tafi ga shagalar mutane da wasa da gafala, da tozarta sallah da wasun wa'ennan.

Ya yan uwa na kada mu warware sakar da muka sa'ka bayan kai komo da muka yi wajen sa'ka ta !

Muji tsoron ALLAH bayin ALLAH, mu kiyaye abunda muka aikata na alkhairi, mu tuba ga kura kuran mu, ALLAH yana gafartawa wanda ya tuba !

Post a Comment (0)