_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(11)
ZAKKAR SHANU:
Fahimtar Mazahabobin nan hudu ta hadu a kan cewa,
nisabin shanu yana farawa ne daga talatin.
Don haka ida shanu ba su kai talatin din ba, to babu zakka.
Toh Amma idan suka kai talatin din, za a bayar da namijin sa ne,
wanda ya cika shekara biyu.
yayin da suka kai arba’in sai a bayar da saniya ‘yar shekara hudu.
Daga nan sai a bayar da saniya ‘yar shekara hudu.
Daga nan kuma sai a komo lissafin arba’in ko talatin.
Watau a kowace arba’in a bayar da ‘yar shekara hudu.
Ko A kowace talatin kuma a bayar da namijin sa wanda ya cika shekara biyu.
(Duba Hashiyatul Adawi, na Ash-Sheikh Aliyu As-sa’idi al-Adawi, juz’I na
(1, sh: na 438 – 441).
Wan nan Shine NISABIN Zakkar Shanu Wallahu A'alam,
_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*
Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
