*_TA YI ZINA, TANA IDDA?_*
*Tambaya*
Malam bazawara ce take iddan saki, amma tana zina, ya matsayin iddan nata?
*Amsa*
To 'yar'uwa, ına rokon Allah ya kare mu daga zamewa, da kuma yin abin da zai kai mu zuwa ga fishinsa, idan kın yi zinar ne bayan kin yi jini daya ko na biyu, kafin ki shiga na uku, to malamai sun yi sabani akan haka, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi istibra'i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama daidai ita ce: kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi istibra'i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar istibra'i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki.
Yana daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu daya ce, jinsinsu guda ne, to daya za ta shiga cikin daya, kamar wacce ta yi jima'i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda daya ya ishe ta a karshen hailarta.
Allah ne mafi sani.
Duba: Majmu'ul fawa'id na Sa'ady shafi na: 141.
24/3/2016
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.