FALALAR ALLAH



FALALAR ALLAH 
🍃 Ka tuna cewa: Falalar Allah tana da girma kuma tana da yawa da fadin da hankalinka bai isa ya iya ganota ba.

🍃 Kamar yadda ya baiwa waninka falalar yana kuma da ikon da zai baka irinta koma wacce tafi ta, kuma yana da ikon ya hanaka.

🍃 Kar ka sanya zuciyarka cikin damuwa, kar ranka yayi ta baci akan kaga Allah ya baiwa waninka wata falalar da kai baka da ita, idan ka waiga wani bangaren, da sannu zaka ga kaima ya baka wata falalar da bai bashi ba.

🍃 Abinda ya dace shine: Ka Roki Allah daga Falalarsa, insha Allahu zai baka fiye da yadda kake zato, kuma mafi alkhairi gareka matukar rabonka ya tsaga.

🍃 Ta yiwu abinda kake hange da burin samuwarsa gareka saboda kaga waninka dashi sai kaga ba alkhairi bane a rayuwarka ta duniya da lahira.

🤲🏻 Allah ya kara rufa mana asiri duniya da lahira kuma Ya yarda damu da ayyukanmu, ya bamu kyakkyawa anan duniya da lahira.

✍ Rubutawa:
Abu Nu'aym Rismawy
Post a Comment (0)