_Fitowa ta 5 (cigaba)_
*LABARIN SOYAYYAR WATA YARINYA🕊️*
A fitowa ta 4 munji irin yanayi da wannan bawar Allahn ta shiga, kuma munji yadda mahaifinta ya dauki abun da zafi, har ta kasance itace take bashi hakuri akan abin da ya faru, to take ce mana: Ban sani ba ko za mu sake samun damar magana dashi ba ko yaya? . Sai take ce mana: _Amma kun san me ya faru bayan nan?_
💔Tace: Yawan tunani da damuwa ba su bar ni na iya yin barci cikin sauƙi ba, duk lokacin da na kwanta, sai in ta tunaninsa. Na samu labari daga wajen babban abokinsa cewa ya yi aure tare da wata yarinya har na yarjejeniyar shekara biyu kuma ya samu shaidar zama ɗan ƙasar Amurika. Na kan tambayi abokinsa game da mahaifiyarsa cewa yaya take? Shi kuma abokin na sa yakan tambaye ni - ke kuma fa yaya kike? Nakan yi murmushi nace Alhamdulillah, ina nan lafiya.
💔Kwanaki suna ta tafiya amma ciwon dake zuciya yana nana, duk da dadewar lokacin da abin ya faru amma na kasa manta komai. Amma sai dai idan mutum yayi ƙoƙari sosai na manta abubuwan da suka faru a rayuwarsa to yakan manta idan ya dage sosai, kuma gaskiyar magana ita ce - mafi yawan abin da muke son mantawa da shi ba ma iya manta shi cikin sauqi saboda abin da muka fi mayar da hankali akai shine raunin da muka samu amma ba darussan da ke ciki ba wanda zasu jagorance mu zuwa ga canji a rayuwar mu ba. Don haka na dage na bar tunaninsa kamar yadda yake kuma na rungumi kaddarata. Ban tsane shi ba kuma ban tuhume shi da cin amana ta ba, saboda ni ce na ƙaunace shi kuma na so shi fiye da yadda ya cancanta na so shi, kuskuren duka nawa ne. Don haka na binne duk wasu tambayoyina da zargin da nake masa. Kuma na yi ƙoƙarin fahimtar hikimar dake cikin jarabawata sannan na yanke shawarar cewa duk yadda rayuwata zata kasance, to zan bar rayuwar sa ta kasance cikin farin ciki tare da ƙauna a koyaushe.
💔Amma ban san abin da ya sa ya kira ni ba kuma har yake bani labarin aurensa a taƙaice ba. Na kasance mutum mai kyakkyawan sauraro koyaushe. Don haka na tsaya na saurare shi har yake fadamin yadda ya yi auren da yarjejeniya ta shekara 2 amma yanzu yana cikin tsananin soyayya da farin ciki shi da matarsa. Don haka zasuyi rayuwar aurensu ta hanyar gaskiya har zuwa karshen rayuwarsu kuma yana matukar buqatan fatan alkhairina akan hakan. Na shiga tunani - auren yarjejeniya na shekara biyu kawai ya ma fi soyayyar shekara bakwai da nayi masa. Wani hawaye mai zafi ya taru a kusurwar idanuna amma na taya shi murna tare da yi musu addu'oina. Ya katse kiran yana cewa '' Allah Hafiz ni 'kuma ina tsaye a nan, ina rike da waya tare da yin nadama.😔
💔Shekaru 10 suka shude kuma ba mu ga juna ba. Muryar da take da daɗi da zurfin sauti a kunnena yanzu itace wacce sam bana jin ta. Alkawuran da na dauka na cewa zan ƙaunace shi har abada yanzu babu su. Duk wannan tunanin duk sun gushe kuma ina cikin lafiya yanzu. Amma ku dan Dakata, 🤚 kada kuje ko'ina. LHar yanzu akwai sauran abin da ya rage da nake son faɗa muku ku saurara. 👇
*✍️BAYANIN MAI RUBUTU*
💔 Tadaaa ... don haka wannan shi ne karshen ainihin labarin wata yarinya mai kirki da sanin yakamata wacce ya faru da ita a gaske. Wannan labarin gaskiyane amma ba komai bane gaskiyane aciki saboda nima sai na rubuta shi a nawa hanyar yadda za'a iya karantawa tunda ban san kowane 'karamin bayani game da hakikanin yadda' yarinyar take ji ba wanda ban taba haduwa da ita ba (kamar kukan da tayi, tausayi, dariya dss wnn duk bazance ga yadda tayi ba na rubuta ne kawai) amma shi saurayin nata na sha haduwa da shi sau da yawa.
💔Koyaya ne ma dai, naga cewa labarinta zai iya zama darasi akan mu mu mata, kuma gargaɗi ne ga sauran yan mata akan kada su bari kowane mutum ya yi wasa da rauninsu da soyayyarsu. Hmm Soyayya? ☹️ Ina matukar shakkar irin wannan son da kaunar da mafi yawa ma haramun ne. A gare ni (ko a waje na), 'Masoyi' za a iya kwatanta shi ne da sigari - da zaki riƙe ta da karfi, da zaki rike ta kusa da leɓenki, kina tunanin wannan sigarin zata kasance tare da ke amma a karshe komai sai ya juya ya koma zuwa toka.☹️ Sanan ta kumbura miki huhunki ta sa zuciyarki tayi baki ta sa miki baƙin ciki tare da cututtukan mutuwa. A karshe ta barki aciki (to haka sairayin yanzu yake). Don haka yan uwana mata ayi hankali.
*Yar uwarku: Maha✍🏻*
_✍️Wannan shine karshen wannan labarin namu, kuma kofar muhawara a kansa a bude take, zamu tattauna akansa a cikin zauren mu na *FILIN MUHAWARA* in shaa Allah, sannan menene tunaninku game da maganar karshe ta ita marubuciya??🤔 anya duka samari suke haka kuwa? Sannan wane darasi kuka dauka acikin wannan labarin, kuma shin laifin waye? Shin na yarinyar ne da ta so shi da yawa fiye da yadda ya cancanta? Ko kuma dai na sa ne da ya yaudareta bayan soyayyar shekara 7???_ 🕊️
_🕊️•••> Zamu hadu a sabon labarinmu mai taken .... ✍️_
✍Rubutawa: *Yar uwarku Muhazzabin*
📝Fassarawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*
03/04/2020.
Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
