MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 12


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(12)

ZAKKAR TUMAKI DA AWAKI:

Shi kuwa nisabin awaki da tumaki yana fara wa ne daga arba’in (40).

Watau wanda ya mallaki awaki da tumaki ba zai fara fitar da Zakka ba sai sun kai arba’in.
ga dai yadda tsarinsu yake:

NISABINSU 
Daga tumaki/awaki 40–120 sai a bada Akuya/tunkiya(1)

Daga tumaki/awaki 121-200 sai a bada Akuya/tunkiya(2)

Daga tumaki/awaki 201–300 sai a bada Akuya/tunkiya 3

Idan suka wuce haka, to kowace dari sai a bayar da akuya ko tunkiya daya.

(Duba littafin da ya gabata sh: na 442 – 443.)

Wadan nan sune nisabin zakkar Awaki da kuma Tumaki.

Wallahu A'alam

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)