<<<MUTUWA TA ISA WA'AZI>>>
MUTUWA ITACE MAFI GIRMAN MUSIBU.
Mutuwa daya ce daga cikin mafi girman musibu.
Domin hakika Allah madaukaki ya ambaceta musiba. A cikin fadar sa. (SANNAN SAI MUSIBAR MUTUWA TA SAME KU.)Suratul ma'ida. Ayata 106.
Idan bawa ya kasance mai da'a sai mutuwar ta sauka gare shi, to zai yi nadamar cewa da dai ya kara ayyuka kyawawa fiye da yadda yayi. Idan kuma ya kasance mai mugun aiki, to zai yi nadamar akan sakacin da yayi. Kuma zai yi gurin komawa duniya domin ya tuba zuwa ga Allah madaukaki. Ya kuma yi sabon aiki na kwarai. Sai dai kuma hakan ba zai samu ba. Allah madaukaki yace (kuma idan sun nemi yarda ta hanyar komawa duniya domin su gyara, to baza su zama cikin wadanda ake yardarwa ba) suratul fussilat: Ayata 24
Haka kuma Allah (s.w.t) yace.[[HAR IDAN MUTUWA TAJE WA DAYAN SU SAI YACE" YA UBANGIJI KU MAYAR DANI DUNIYA DOMIN TSAMMANI INYI AIKI NA KWARAI CIKIN ABINDA NA BARI. A'a lallai ne ita wata kalma ce shine mafadinta. ALHALI KUWA ABAYA GARESU AKWAI WANI SHAMAKI HAR RANAR DA AKA TAYAR DASU]] suratul al-muminun; Ayata 99- 100
