SHIN BA ZA MU YI IMANI BA?
Halittar baros (virus) ita ce halitta sananniya mafi qanqanta a cikin halittu masu rayuwa a doron qasa, da wannan halittar kaďai Allah Ya turo mana jarabawar da ta girgiza duniya gaba ďayanta, har da qasashen da suke taqama da ilimin kimiyya da fasaha tare da zaratan dakarun yaqi da miyagun makamai, amma Allah Ya turo masu qanqanuwar halitta wacce ido ma ba ya iya gani duk ta addabe su ta hana su saqat, wallahi wannan aya ce daga cikin ayoyin da Allah Yake buga misali da su, amma babu mai fahimtar hakan sai mai hankali irin na addini.
Annoba azaba ce ga dukkan wanda ya kafirce wa dokokin Allah Ya riqi wani abin dogaro ba Allah ba, haka kuma rahama ce ga dukkan wanda Ya kyautata imani da Allah kuma ya miqa ragamar al'amuransa gare Shi (Allah).
'Yan uwa tabbas wannan annoba za ta iya kasancewa sakamako ne na miyagun ayyukanmu, don haka mu duqufa da tuba tare da neman gafarar Ubangiji, in shā Allah za mu katangu daga wannan masifa.
.
Ya Allah Ka kare mu da iyalanmu da dukkan al'umar musulmi daga wannan cuta mai halakarwa 👏🏾😭
.
*Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*
*👨👩👦👦IRSHADUL UMMAH.*
*+2348166650256.*
https://www.facebook.com/896785910406825/posts/2793657560719641/?app=fbl
