NIJERIYA INA MUKA DOSA?

*Najeriya ina muka dosa?*

Fira ce tsakanin Bafulatanin daji da wakilin gwamnatin jihar Zamfara. Duk wanda ya saurare ta ya san cewa, arewacin Najeriya muna cikin halin ban tausayi. Abinda zai faru gobe kuma Allah mai cikakken sani ne kawai ya kebanta da sanin sa.

*Ra'ayina:*
1. A gajeren zango:
Yadda aka nemi zaman lafiya da yan ta'addan Niger Delta ba don ana so ba, don dai sanin cewa gwamnati ba ta iyawa da su, a shirya makamancin haka da hillani.
2. A dogon zango:
a) A inganta rayuwa da ba da ilimi ga makiyaya mutanen daji.
b) A samar da hanyar inganta tsaro da jami'an tsaro.

Ya Allah! Ka dube mu da rahama, ka kawo mana dauki, ka kare jinainanmu da mutuncinmu.

Post a Comment (0)