MU KOMA GA ALLAAH

*MU KOMA GA ALLAH😭😭😭.*


1 Dazaran katashi zaka bude Data don gani sakon duniya. Amma Sallar Asubah cikin Jam'i tagagareka. *Mu koma ga Allah.*


2 Kana iya minti 90 cikin kallon ball idan anyi rashin sa'a atafi extra-time. Amma Sallar farilla tagagareka cikin Jam'i don kallon ball. *Mu koma ga Allah.*


3 Kana iya haddace handout don ganin kaci jarrabawar duniya ta dan adam, Amma baka iya haddace surah daya ta Alqur'ani don guzurin lahira. *Mu koma ga Allah.*


4 Kanada halin kyautar mota don neman suna, Amma baka da hannun kyautatawa gajiyayyu da marayu don neman lahirarka. *Mu koma ga Allah.*


5 Kanada lokacin musu, Amma bakada lokacin yiwa Annabi salati. *Mu koma ga Allah.*


6 Kanada kudin sayan mota da sutura ta alfarma, Amma sayan Sinsiya ta sharar dakin Allah tagagareka. *Mu koma ga Allah.*


7 Kanada lokacin karanta jarida, Amma bakada lokacin karanta maganar mahaliccinka. *Mu koma ga Allah.*


8 Kana iya kuka don Asarar abun duniya, Amma tuna azabar kabari yagagareka. *Mu koma ga Allah.*


9 Kanada lokacin kallon season film, Amma sada zumunci tagagareka, don neman haye siradi. *Mu koma ga Allah.*


10 Kanada lokacin zuwa ko inane don neman abun duniya, Amma neman ilimin sanin mahaliccinka yagagareka. *Mu koma ga Allah.*



11 Kaine jagora wajen zalunci da cin dukiyar al'umma, Amma kiran sallah (Ladanci) Abun kunyane agareka. *Mu koma ga Allah.*


12 Ka zabi rayuwar duniya fiyeda ta lahira, bayan bakasan yaushe zaka mutu ba. *Mu koma ga Allah.*



*👉🏼NAZARI NA MUSAMMAN.*


1 Idan arziki ne yasanya kabijirewa mahaliccin ka, to yau ina *Qarunah?.*


2 Idan zallan sabon Allah kakeji dashi da shagaltuwa, to yau ina *Fir'aunah?.*


3 Idan zalunci kasa agaba to yau ina *Hamana?.*


 *👉🏼YAKAI DAN'WA AMUSULUNCI KASAKE TUNANI.*


1 Talauci baya hana dautar Allah. Tuna da tarihin *Annabi muhammad (S.A.W).*


2 Idan hassada akema, Tuna da tarihin *Annabi yusuf. (A.S)*


3 Idan radadin ciwo zai sakamanta da Allah tuna da tarihin *Annabi Ayuba. (A.S)*


4 Idan zallan kinka ake kan gaskiya, tuna da tarihin *Manzon Allah (S.A.W).*


5 Idan wani abune yadameka, Waraka na cikin *Alqur'ani.* Karanta kabarwa Allah komi.




*@MU KOMA GA ALLAH.*
 KARANTA KATURAWA WANI DON SHIMA YAKARU, ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA (AMEEN).*


Post a Comment (0)