RAYUWAR AURE SIRRI CE

*Rayuwar Aure sirri ce*

Wata mata da mijinta sun ziyarci gidan zoo, sai matan taga biri yanata wasa da matarsa, abun ya
matukar burgeta, sai tace ma mijinta, kai kalli soyayya irin wannan rayuwa cike take da jin dadi da
dacewa.

Lokacin da sukayi gaba zuwa bangaren zakoki
kuwa, sai ta ga namijin zaki ya kwanta nesa da
matarshi yayi shuru sai tace; Kai wannan labarin
soyayyace me bakanta zuciya, wannan kalan
soyayyan takan kawo gajiya, cike take da damuwoyi.

Sai mijinta ya kalleta yace, ansa wannan kwalban a
hannuna ki jefi matar zaki da ita, lokacin da ta jefa
sai zakin ya zabura ya mike yayi ihu, yana neman wacce ta taba masa matarsa don daukan fansa.

Sai ya bata wani dutse yace muje ki jefawa matar biri, sai suka tafi, tana jefawa matar birin, sai birin ya ruga a guje yana neman maboya kada shima
abin yazo kansa.

Sai mijinta yace mata kingani, kada ki rudu da abinda mutane suke nunawa a gabanki, karma ki yaudari zuciyarki akan haka.
Akwai mutane da suke yaudarar mutane da yanayi
na karya.

Kuma akwai mutane dasuke boye tsananin so da
suke maka a cikin zuciya, alhalin zuciyar cike take
da so da kaunarka.

*Akwai Darussa acikin wannan labari...*🖊

Post a Comment (0)