HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 5


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*

 ```// 005```
.
GUJI YAWAN KAWO HANZARI
Wasu za su iya yin duk abinda ake buqata, hasali ma su ne kawai za su iya yi din, amma yawan koke-koke ko kawo hanzari shi zai ruguza su ya bata tafiyar gaba daya, wani kana tuntubarsa a kan wani abu mai matuqar mahimmanci a rayuwarsa sai ya ce maka mu yanzu ai mun girma ya za a yi mu iya? Hanzarin dai shi ne yawan shekaru, akwai kuma wanda zai ce gaskiya ba zai iya ba saboda qarancin wayewa, ko ilimi, ko kudi, ko shekarun, ko dai wani abin na daban, matuqar mutum ya ce ba zai iya yin abu ba saboda wani dalili da ya dogara da shi, da wahala ka ga ya motsa, ya haqura da nasarar kenan.
.
Wani maqwabcimmu yake cewa "Lokacin da muka shiga JSAIE (Junior Secondary School for Arabic and Islamic Education) ba mu san komai ba, gaskiya ni ko baqaqen da Larabci ban iya ba, mun dai yi karatun allo kuma mun sauke, mun haddace wurare da dama amma sunan Nahawu ma lokacin na fara ji, don haka muka nemi wani malami da zai taimaka mana, shi ya koyar da mu littafai da yawa, a dalilinsa muka fara sanin inda aka dosa, mun ga sa'o'inmu a ajin, da qanninmu da ma wadanda suka haife mu ba yayyimmu ba.
.
Mun yi shekara daya cur tare da malam muna qaruwa, tsakani da Allah ba abinda muka sani shi ya riqa dora mu a kan hanya, a shekara ta biyu ya ce mana shi fa iyakarsa kenan sai dai mu nemo wani malamin, hankulimmu ya yi matuqar tashi, haka dai muka yi ta bundun-bundun mu fada nan mu tashi can, cikin ikon Allah muka shekara shida muka kammala karatun, muka wuce kwalejin share fagen jami'a muka samo kwalin diploma, muka dawo gidan da muka zauna muna tuna baya, cikin ikon Allah a ranar sai ga malamin namu ya yi sallama ya shigo.
.
Abin mamaki sai ya sami wuri a qasa ya zauna bayan mu muna kan kujeru a zaune, sai ya ce wai ya zo neman sani ne, haka dukammu ukun muka yi qasa, ya ce wallahi shi tun daga shekara ta biyu ya rabke ya kasa ci gaba, yana ganin ya girma ga kuma qarancin abubuwan masarufi, mu ga shi Allah ya taimake mu har mun kai ga Diploma, tsakani da Allah ba don neman sani ba da ba zai zo ba, saboda haka mu koma kan kujerarmu in ta so in mun ba shi amsa ma sauko qasa, muka ce masa wallahi in dai yana qasa ba wanda zai hau kujera.
.
Da dai ya ga da gaske muke sai ya hau din kuma ya umurce mu da mu hau, da farko mun qi, amma da muka ga zai shiga wani hali muka hau, sai bayan mun gama sai ya yi mana nasiha da cewa kar mu taba samun raunin gwiwa a kan karatu, da ma duk abinda muka shiga, na san dai yana yin wata sana'ar da tun farko muka san shi da ita, mu kam yanzu muke tasowa amma a dalibansa wasu sun zama marunbuta, wasu malaman jami'a wasu manyan 'yan siyasa, wasu 'yan kasuwa da malaman muslunci, a sa'o'inmu ni na san wadanda suka zama manyan sojoji, 'yan sanda, alqalai, lauyoyi, malamai a jami'u da sauransu, akwai wadanda suka koma suna koyarwa a zaurukan gidajensu ana ba su sadakar Laraba".
.
Wasu tabbas sun sami karayar zuciya ne a dalilin qarancin kudi, wasu za su ce maka ba sa ganewa, akwai wanda muna karatun ya arce abinsa wai shi aure yake so, ya yi auren amma ya kasa dawowa fagen da yake ciki har abokan tafiyar nasa suka yi masa nisa, sai ya gan su ya yi ta sha'awa, akwai wanda ya qi karatun wai za a maida shi dan Izala, a daidai lokacin mu kammu muna kukan cewa Dariqar ake koya mana, don littafan tauhidin sam ba sa taimakon 'yan Izalan a aqidunsu, amma duk da haka muka yi haquri muka dage har muka gama, kuma ba abinda ya shafi aqidummu, shi kuma har yanzu yananan yau kamar jiya.
.
Akwai kuma wani bawan Allah da muka zauna wuri guda, yana HND a bangaren kimiyyar noma da tsire-tsire, muna koyarwa wuri guda, ya ba ni shekaru da dama kuma ya fi ni wayewa da sanin kan rayuwa ta ko'ina, a haka na je na yo digirina na farko a waje, na dawo na ba shi shawarar ya canja layi kawai ya dawo bangaren koyarwar tunda yana da sha'awa, na yi dace ya manta da shekarunsa da wayewarsa ya koma makarantar, cikin 'yan shekaru ya samo kwalin Digirin shi ma, ya dora digiri na biyu, a maganannan da muke yi shi ke jagorantar wani babban kwaleji.

Rubutawa:-Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)