*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//03📿*
*DALIBIN ILIMI*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Akwai abubuwa da dama da suka yi kutse cikin al'amuran al'umma da kaikomonsu wadanda za mu ce ba wasu nassoshi qarara a shar'ance da suka yi magana a kai koda kuwa ita shari'ar ta riga ta yi bayani a nassance ko wani fiqihunce ko ta kusanto da ma'ana amma ba kowa yake iya hararo hakan ba in ba gogaggun malamai masu koyarwa ba, kenan wanda yake jin harshen da nassi ya zo da shi ba zai iya hararo irin wannan hukunci na nassi a cikin sauqi ba, qila sai an yi masa bayani, amma sai ya ce "Babu" kai tsaye don bai gani ba bai kuma tambaya ba, yin hakan kuskure ne.
Duk wani dalibin ilimi mai tasowa, ko mai karantarwa yana da buqatar bin wadannan nassosi na shari'a gwargwadon yadda malamai magabata suka yi magana a kai daidai fahimtarsu, zai gina fahimtarsa ne a kai daidai da tasu, wannan ya sa karanta littafansu ko zama a gabansu ko gaban dalibansu suka zama wajibi, da haka ne zai ga irin yadda suka yi ma'amalla da mas'aloli, da irin hanyar da suka bi wurin fidda hukunci, tabbas sun yi aiki ne a kan nassosi ba qago wasu nasu suka yi daidai da zamaninsu ba.
Da kallon gurabun magabata ne dalibin ilimi zai auna fahimtarsa da ta magabatansa a kan mas'alolin da za a iya karbarsu ko a mayar, amma kamar zancen cewa yanzu akwai wasu lamura sabbi wadanda magabatanmu a baya can ba su san da su ba kuma ba su yi magana a kai ba nan kam akwai buqatar abinda zai taimaka mana wurin kyautata fahimtarmu da nassin, tabbas akwai bayanai masu dimbin yawa da magabata suka yi magana a kai wadanda sun yi daidai da lamuranmu na yau, amma yanayin bayanan da zarafin da mu muka sami kanmu ba za mu iya binsu cikin sauqi ba.
Dole muna buqatar malaman da muka amince da su su yi mana bayani dalla-dalla da za mu iya kafa hujja da shi, ta wurin bin bayanan magabatannan ne za mu sami wanda ya fadada, ko ya taqaita a kan mas'alolin da za mu iya kwatanta su da abinda yake faruwa a yau, mu kuma sami amsar duk abunuwan dake rikitar da mu a baya, a zahiru cikin irin magabatannan za ka sami wasu wadanda suka yi fice wurin fahimta da zaqulo mas'alolin dake daure nassosi da lamuran dake faruwa a rayuwar yau har ma ya kasance ba lamari mai daure kai a yau wanda ba su yi magana a kai ba.
Kenan duk wani dalibin ilimi yana da buqatar komawa ga magabata, ya karanta littafansu ya zauna a gabansu ko a gaban dalibansu ko wadanda suke da gamayya da su don sanin fahimtarsu game da mas'alolin addini, in dai wannan zai samu to zai yi wahala ka sami qaramin dalibin ilimi ya iya bude bakinsa don sukar wani babban malami wanda duniyar Nigeria ko Arewacinta ta yarda da iliminsa ko da'awarsa, da wahala ka ji dan qaramin dalibin ilimi yana bidi'antar da manyan malamai ko jefa su cikin wasu qungiyoyin addini kamar Ikhiwananci ko Tabliganci da sauransu
Domin sanin yadda dalibin ilimi zai yi mu'amalla da wadanda yake ganin kamar sun saki hanya akwai buqatar bin wasu manyan ginshiqai da sanin yadda zai yi mu'amalla da su, ba wai fahimtarsa kawai ta zama ma'aunin da zai iya ware mabiya Sunna da 'yan bidi'a ba, bare kuma har himmarsa a addini ta qare wajen tantance waye na qwarai waye bara-gurbi, ya manta da sauran abubuwan da suka shafi hukunce-hukunce wadanda malaman da yake bidi'antarwa kullum aikinsu kenan wurin gyara wa al'ummarsu 'yan kura-kuren da suka sami kansu a ciki.
GINSHIQI NA FARKO
*KYAUTATA NIYYA*
Kyautata niyya wani abu ne da ya zama wajibi ga duk wani aiki da ake qoqarin yinsa don neman kusanci ga Allah SW, Annabi SAW yana cewa "Babu wasu ayyuka da za a yi sai da niyya (Buhari da Muslim)" don haka hatta tattaunawa da za a yi da wanda ake ganin ya saki hanya ko raddi a maganganunsa lamari ne na neman kusanci ga Allah, wanda ya zama dole ya kasance akwai kyautata niyya, manufar ta kasance gyara kuskuren ne ta wurin fito da abinda ya dace, wanda ya yi daidai da shari'a.
Ba wai qoqarin kunyata abokin tattaunawa ko qasqantashi a gaban mutane ko almajiransa ba, ba kuma fito da kai ga mutane yadda za su san cewa kai fa masani ne ba, ko ka sami shuhura a wurin mutane da cewa kai fa qi fadi ne matuqar za a tattauna da kai a kan lamuran da suka shafi addini, in mutum ya kasance manufarsa kenan tabbas zai riqa samun matsala ciki har da wadanda fahimtarsu ta shari'ar take daidai, sannan sai ya yi qoqari ba kadan ba wurin kauce wa riya, ita kuwa bata ayyuka take yi gaba daya.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*