TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 2


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//02๐Ÿ“ฟ*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

*SABANIN SHUGABANNI*

Tabbas akwai tashin hankali in ka dubi sabanin dake tsakanin malaman jama'a, ko masu wa'azinsu, ko masu hukunci a shar'ance gwargwadon yadda aka sami rabe-raben qungiyoyi zuwa wasu:-

1) Idan muka dubi masu riqo da sunnar sosai za mu ga akwai sunayen dake raba su zuwa wasu rukunnai koda aqida ba ta raba su ba, kamar ka dubi masu qara As-salafi a qarshen sunayensu, ko masu tafiya a qungiyar Izala ko qoqarin bambance Izalar Kaduna da ta Jos, koda a ce sabanin bai kai ga aqida ba amma akwai bambancin sunaye, shi kuma zai iya nuna bambancin jagoranci ko koyarwa.

2) A dariqu kuwa mun ga yadda aka sami 'yan Faila, ga 'yan haqiqa da suka kunno kai, banda qananan bambance-bambance na waliyai ko shugabanni, wadanda suka sa hatta taron tunawa da Inyasi (H) din wasu na zuwa yankuna, wasu kuma na yin nasu a Abuja.

3) Gidan Qadiriyya mun san akwai 'yan Kogo, a taqaice dai akwai 'yan bambance-bambance dake tsakanin kowa, wasu na jagoranci ne kawai, wasu na shiryarwa, wasu kuma sabani ne ma babba wanda babu yadda za a yi da shi, maganar ba cewa take lallai a hadu ba, amma a yanzu mu yarda cewa akwai wadannan 'yan bambance-bambancen a tsakanin mabiya ko su malaman kansu masu shiryarwar.

Tunda wannan sabanin ya bayyana sosai, qila ba abu ne mai sauqi ba a ce manyan malaman dariqa da na Izala za su iya fahimtar junansu su tafi tare duk da mun sani cewa rabuwar masallaci da musayar yawu a Nigeria bai hana haduwa a Saudiya a yi bautar Allah tare komai a yi iri daya, qila ma a zauna a yi hira ko a yi wa juna ba'a, wasa da dariya ko in ta kama a yi salla tare a bayan wani ko a bayan limamin Makkah ko na Madinan da muka san shi ma aqidar bin Qur'ani da Sunnan ce gareshi, amma zai iya yuwuwa a yi nazarin sabanin Izalar Jos da ta Kaduna tunda ba bambanci ne mai girma ba, ko a yi nazarin fahimtar matasa masu zafin nama dake raina qoqarin magabatan, a kowace qungiya ma a yi nazarin irin wannan bambance-bambancen.

A da in aka sami sabani tsakanin malamai za ka taras akwai tazara mai nisan gaske a tsakaninsu, wani sa'in littafansu ne kawai za su iya nuna muku irin sabanin da aka samu, shi ya sa akan zauna tare ba wata hayaniya ko rashin fahimtar juna a tsakani, amma yanzu akan qalubalanci juna gaba da gaba kowa da dalibansa wadanda suke ganin shi ne da gaskiya tun kafin ma ya bude bakinsa, ga wasu hanyoyin na sayar da faya-fayen tattaunawa, ga kafofin sadarwa na zamani, wannan ci-gaba da aka samu ya dada zafafa alaqar al'umma da wadanda suka saba musu a aqida.

Zan ba da misali, shigowar sunna da irin karantarwanta ba su kawo sabani ba kamar yadda aka sami tafsiran manyan malamai biyu wato na Izala da na dariqa a gidan rediyon Tarayya, za ka yarda da haka in ka duba cewa dariqa ba Tijjaniya ce kadai ba akwai Qadiriyya, amma da yake su Qadirawan ba su da murya a rediyon, sai ba a sami fitaccen sabani tsakaninsu da Izala ko Tijjaniya ba, duk da cewa matsalar 'yan qabalu da 'yan sadalu ba boyayyen abu ba ne ga duk wanda ya dan sami shekaru a baya, anan ba cewa muke kafofin sadarwa sun haifar da sabani ba, amma an fahimci sabanin ne sosai ta wurin musayar yawu tsakanin malaman a kafofin sadarwa wurin tafsiransu, ko a wuraren karatunsu da kafofin ke yadawa.

Ta wurin samun bayyanar wannan sabani sai abokan gaba suka sami barakar da za su shiga, ta wurin nuna irin barnar da wadancan suke muku, ku ma fa ya kamata ku rama kafin su gama janye muku mutane, ko nan gaba su sami wasu madafan mulki su hana ku yin ibadarku, ko su yi qoqarin shafeku a bayan qasa, a irin wannan matsayi muna da buqatar nazari wurin gano babban abokin gaba a lokacin, shin shedanin mutun ne da ake kwana tare a tashi ko na aljani ne wanda ido ma bai gani, to koma wanne ne yanzu gyara ta zama dole matuqar aka fahimci cewa akwai kuskure, sai dai fahimtar ina kuskuren yake? Shin mai kuskuren ya yarda kuma zai karbi gyaran? Su wa za su yi gyarar, kuma ya za su yi? Wannan ba magana ce ta rana daya ba, kusan a kan wannan littafin zai kammala da yardar Allah.

Yanzu dai don mu yi kwadayin gyaran dole mu yarda cewa tilas a zaman tare a sami sabani koda kuwa ana tafiyar gaba daya, mu yarda cewa ba zai taba yuwuwa jama'a ta hadu ba tare da bambancin fahimta ba, ko mutum kansa bai isa ya hada mata da yawa a gida daya ko a mabambantan gidaje ba tare da samun sabani ba, kai ba ma zai yuwu a sami mutane sama da biyu suna tafiyar da komai ba tare da wata 'yar matsala ba, wace take abar damuwa ce ko kuma 'yar qanqanuwa, don haka sauran bayani ya rage a zaqulo hanyar da za a bi wajen tafiyar da wannan sabani wanda duk bangarori guda biyu ko fiye za su yarda da ita, wannan hanyar kuwa ita ce aiki da Qur'ani kai tsaye, in ba a iya gano matsalar a ciki ba a koma sunnar ma'aiki SAW, ko bayanan magabatan da duk bangarorin sun yarda da qimarsu da tasirinsu a cikin addini.

Idan aka yi aiki da lafiyayyar hanya ta wurin ma'amalla da wanda ya bar ta za a sami gwaggwabar riba ba 'yar qarama ba wurin magance wannan baudiyar, da kusanto da shi, da qarfafa alaqarsa da mutanen qwarai, da rage mutanen banza a cikin al'umma, masu wannan aiki malamai ne da masu jibantarsu Ibn Taimiyya yake cewa "Da aka sami hukunce-hukuncen da mutane da dama ba su san su ba sai al'umma ta koma ga masu sanar da su, su suka san abinda Annabi SAW ya fadi da manufarsa a kai (Fatawa 20/224)" idan muka lura da hadisin zuwan Jibril AS wurin Annabi SAW ya zo ne don ya koyar da mu addininmu, iya bangarorin da nake magana a kai (Banda Shi'a) sun yarda da ingancin hadisin suna karanta shi kuma suna karantarwa, to ko anan kawai muka tsaya za mu wadatu da izinin Allah SW.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)