*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//04📿*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
*IN BA IKHLASI FA?*
In mai tattaunawa da mai-kuskure ya ga cewa burinsa kawai jama'a su ga cewa ya ci galabar abokin tattaunawarsa, ko qoqarinsa ya kunyata shi ko ya qasqantar da shi a baina ga jama'a to barin tauna-taunar shi ya fi, don ba abinda ake buqata a wurinsa kamar ikhlasi da son kawar da barna da kawo shiriya, an tambayi Ibn Taimiyya game da magana a kan wani sai ya ce "Wanda zai magana game da haka kuma ya san komai to dole ya tsarkake niyya, da zai maganar wani don neman daukaka ko bata mutum to kamar wanda zai yi yaqi ne don jinjina ko riya".
Ya ci gaba da cewa "In kuma ya yi maganar don Allah, kuma ya tsarkake niyya kamar wanda ya yi jihadi ne saboda Allah, kuma yana cikin magada Annabawa, khalifan manzanni (Fatawa 28/235), a Wani wuri yana cewa (Ad-Dawabit Alfiqhiyya p20): "Abinda ke kan mutum da farko shi ne: Ya kasance don Allah yake yi, mufarsa ita ce yi wa Allah SW biyayya, yana buqatar kawo gyara ne gami da tsaida hujja, amma in ya yi don neman daukaka ga kansa ko qungiyarsa, ko qasqanta wani to wannan ya zama neman girma Allah ba zai karba ba, haka idan ya yi don mutane su ji irin qoqarin da yake yi ko a gani a san shi ne wane, to aikinsa ya rushe" wal'iyazu billa.
Da yawan matasa sun sani ko ba su sani ba sun abka cikin wannan matsalar, sannan da za a yi masa raddi ko a bata masa suna ko a ce masa dan bidi'a ko mabarnaci ransa zai kawo masa cewa lallai ya wanke kansa, shedan ya sami baraka kenan, da farko dai don Allah yake yi, sai ga shi ya koma nemo wa kansa nasara, me yuwuwa kuma ya wuce gona da iri ko ya cutar da wancan, ko a hanyoyin sadarwa na zamani abinda yake faruwa kenan, yanzu za ka ga an fara tauna-tauna cikin kwanciyar hankali sai lamarin daga qarshe ya juya a koma zage-zage a yi ta kawo sunayen magabata da la'antarsu ma gaba daya.
Ko rubuce-rubucen da ake yi yanzu masamman a fagen musayar ra'ayi za ka taras kowa yana ganin shi ne da gaskiya mai (Minhajus Sunna An-Nabawiyya 5/254-255) yana cewa "Mafi yawansu yanzu sun koma qoqarin kare sunansu ne ko wani matsayi nasu ko wanke kawunansu, ba suna yi ne don daukaka kalmar Allah ko a koma addininsa shi kadai ba, sai suka koma fushi da riqe wanda ya saba musu a ra'ayi, ko da kuwa shi din yana da hanzari shi ma qoqari yake yi kuma Allah bai fushi da irinsa, sai qaunarsu ta koma ga wanda ya amince da ra'ayinsu kuma yake bin su sau da qafa, koda jahili ne gafalalle maras manufa mai kyau".
Ya ce "Da haka sai ka ga sun koma yabon wandaba kowa ne ba a wurin Allah da manzonsa, su koma aibanta wanda Allah da manzonsa ba su aibanta shi ba, sai ka ga yardarsu ko qiyayyarsu da wasu sun zo daidai da son zuciyoyinsu, ba a kan addinin Allah SW ba" Al-Gazali yake magana kan wanda niyyarsa ta baci ya ce "Yana ganin cewa burinsa shi ne kawo gyara a tsakanin jama'a, amma kuma da a ce mutane za su koma wurin wani da ya fito daga cikin sa'o'insa kuma mutane suna gyara lamuransu a hannunsa sai ka ga baqin ciki da hassada na neman kashe shi, in da wani daga cikin mabiyansa zai yabi wancan nan take za ka ga gaba ta shiga tsakaninsa da shi (Ihya'u Ulumid deen 3/369).
Ka ga anan ba ya son addini ya daukaka a hannun wani kenan in ba shi ba, daukaka yake nema wa kansa da shugabanci, a maimakon addini, wannan ita ce boyayyiyar masifar dake addabar duk wanda yake son shuhura ko kowa ya san shi, malamai da dama suna tsoratarwa game da wannan matsalar wato rashin kyautata niyya, babbar matsalar ita ce a boye abin yake mutane da dama suna fadawa ba su sani ba.
Duk yadda wata qungiya take qoqarin samun nasara a kan wata, ko wani malami a kan wani, ko wani ya yi nufin qasqanta wani don ya saba masa, ko kuma ya qi shiga cikin mabiyansa, ko ya yi niyyar yi masa raddi tabbas niyyarsa za ta bata aikinsa, zai yi wahala ya kauce wa fadawa cikin sabon Allah don a qarshe zalunci zai yi, sannan kau da kai ga laifin mabiyi duk da bayyanar kuskurensa da qin gaskiyar da ya yi, ko kuma watsa karkatacciyar fahimtarsa bayan da shi mutumin qwarai ne kuma yana da iliminsa ba shakka wannan abu ne dake bata aikin mutum, ya kai shi ma ga uqubar Allah SW.
Duk wanda ya qi wata barna, ko ya gyara ta, sai aka wulaqanta shi a kanta ya yi haquri kawai, kar ya yarda maganar ta kai ga wuce gona da iri a kan haqqin wanda santsi ya kwashe shi, bare kuma har ya manna masa abinda bai fada ba, ko ya yi ta kwazazanta barnar da ya yi, don dai kawai ba su yi daidai a fahimta ba ko kuma ya dan tabe shi a raddi da ya yi masa, manufa dai ta kasance ba muzanta mai kuskure ake qoqarin yi ba, gyararsa ake buqata yadda zai dawo daidaitacciyar hanya, muzanta shi bai nufin zai gyara halinsa a shekara goma ko fiye, in ya gyaru kuwa take zai bar abinda yake yi.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*