TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 9


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//09📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

*MAGANAR IBN QAYYIM*

"Baiyuwuwa ga duk wani malami ko mai hukunci ya yi fatawa ko ya yi hukunci daidai sai da fahimtar dayan abubuwa guda biyu:-

1) Sanin abubuwan dake faruwa yau da kullum, fahimtar hukuncin da za a iya tsakurowa, sanin yadda za a kawo hukuncin ta wurin kula da wasu abubuwa masu kama da juna ta wasu fuskokin, har dai a sami abinda ake buqata na ilimi.

2) Wajibcin fahimtar sanin hukuncin shari'a kan abinda ake ciki, wato fahimtar hukuncin Allah SW wanda ya yi hukunci da shi a littafinsa ko a kan harshen Annabinsa SAW dangane da abinda yake faruwa".

Ya ce "Bayan ya san wadannan abubuwa guda biyu, wato abinda ke faruwa da kuma hukuncinsa a wurin Allah SW "Sai ya gwama su ta wurin yin aiki da duk qoqarin da yake da shi, ba zai rasa lada biyu ko daya ba, masani shi ne zai hada masaniyarsa ta wani abu da fahimtar da ya yi da kuma hukuncin Allah SW da manzonsa SAW (At-Turuq Al-Hukmiyya 1/131) marigayin ya ce "Akwai nau'o'i na ilimi guda biyu wadanda suka zama dole ga duk wani mai hukunci".

Ya ce "Su ne: Sanin hukunce-hukuncen da aka tanadar ga duk abinda ke faruwa da kuma sanin ainihin abinda ke faruwan, da irin dabi'un mutane, ta yadda zai iya rarrabewa tsakanin mai gaskiya da maqaryaci, da mai yi don gyara da mabarnaci, daganan sai ya hada wadancan abubuwan guda biyu, ya ba wa abinda yake faruwa hukuncinsa na shari'a, ba zai sanya shari'ar ta saba wa ainihin abinda yake faruwa ba (At-Turuq Al-Hukmiyya 1/3).

Ibn Qayyim Al-Jauziy ya tabbatar da haka a littafinsa na (I'ilamul Muwaqqi'in an Rabbil Alamin) inda yake cewa: Babi a kan sauyawar fatawa da canjawarta gwargwadon canjin zamani, wuri, yanayi da niyya da sake gina shari'a a kan maslahar bayi a rayuwa da makomarsu" wannan babi babba ne qwarai mai matuqar amfani wanda rashin saninsa aka yi ta fadawa kuskure a lamuran Shari'a, aka shiga qunci da wahala da dora wa kai abinda Allah bai dora wa kowa ba.

Wanda shari'a babban abinda ta fi baiwa mahimmanci shi ne abinda zai amfanar, ba za ta zo da abinda zai wahalar ba, tushenta ainihi a kan hukunci ne da duba sauqi ga bayi cikin rayuwarsu da makomarsu (I'ilamul muwaqqi'in 2/425), a lokacin da Shafi'i ya bar Iraqi ya koma Masar ya ga lamura ba kamar yadda suke a can Iraqi ba, sai ya dan daidaita wasu abubuwan a mazahabarsa gwargwadon canjin da ya samu na wurin zama da ainihin mutanen da zai rayu da su a yanzu, kenan hatta wanda za ka yi tauna-tauna da shi ka dubi wannan sashin, ka yi masa hanzari.

Daliban ilimi a yau littafin wani malami dake zaune a masar ko saudiya ko wata qasa cikin qasashen Larabawa za su dauka su karanta sai su dubi wani daga cikin malamansu dake zaune da mutane irinsu su yi masa hukuncin cewa ya saki hanya ya zama dan bidi'a don ya ce kaza, in ba su tura shi mu'utazilanci ba to dan ikhwan ne, koda kuwa ba su da wata hujja a hannu wace za ta tabbatar da haka, hujjarsu ya ce kaza rana kaza a wuri kaza, littafin wane, ko malam wane dake zaune a qasa kaza ya ce wanda ya fadi kaza to kaza ne, Allah ya kyauta.

*GINSHIQI NA TAKWAS MATSAYIN FATAWAR WANI*

Ba a kawar da qoqarin da wani ya yi gaba daya wurin fatawa sai in ya saba wa ingantacce kuma bayyanen nassi, in mutum na yawan karance-karance zai taras da wurare masu dama da malamai suka yi ta samun sabani a cikinsu, kowannensu za ka taras akwai abinda ya ja hankalinsa wurin tabbatar da wani hukunci, in dai ba a sami hukunci bayyananne ingantacce da ya saba masa ba ba za a kawar da nasa gaba daya ba, don ba wani ma'asumi da za a ce wannan za a karba -da ra'ayi- ba wancan ba, Annabi SAW ne kadai ba ya tabbatuwa a kan kuskure.

Ibn Taimiya ya ce "Idan aka ga wata mas'ala ba hadisi ko taruwar malamai a kai za a iya duba fatawar wani ba za a ce kar a yi aiki da ita ba (Al-Fatawal Kubra 9/113), a lokacin da Ibn Taimiya yake bayanin hanyoyin Ahlus sunna da na 'yan bidi'a yake cewa "Mas'alolin da al'umma suke jidali a kai na aqida da fiqihu in ba a mayar ga Allah da manzonsa ba gaskiya ba za ta bayyana ba sai dai su yi ta jayayya ba tare da fahimta ba.

Zamuci gaba insha Allah.


*Gabatarwa:Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)