*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//10📿*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Ibn Taimiyya ya ci gaba da bayani dangane da tauna-tauna a tsakanin juna yake cewa "Idan Allah ya yi musu rahama sai ka ga wasu sun sake wa wasu sun karbi fahimtarsu ba tare da an abka wa juna ba, kamar dai yadda abin ya riqa faruwa a zamanin sahabbai, lokacin halifancin Umar RA da Usman RA, sukan yi ja-in-ja a wasu mas'aloli amma daga bisani sai ka ga wasu sun sake ba tare da wuce gona da iri ba, in kuwa Allah bai so yi wa mutane rahama ba sai ka ga an sami mummunar husuma har ka ga an fara musayar yawu, wani ya kafurta wancan ko fasiqanta shi, ko ma ya sa a tsare shi, ko a ba shi kashi ko ta kai ga kisa.
Wannan dabi'ar 'yan bidi'a ce da azzalumai kamar Khawarijawa (Boko haram) da makamantansu" in ji shi, ya ce "Wadannan su ne suke abka wa mutane don kawai sun saba musu a fahimtar wasu mas'alolin addini, ba su kadai ba akwai wasu ma masu son zuciya sai su qirqiro wata bidi'ar da ba'a san ta ba, kuma su kafurta duk wanda ya saba musu a kanta, haka 'yan Shi'a, Mu'utazilawa, Jahamawa da sauransu suke, wadanda suka kawo zancen cewa Qur'ani halittacce ne daga cikin wadancan ne, su suka zo da maganar, daga bisani kuma su kafurta duk wanda ya saba musu, su qwace masa dukiyarsa kuma su azabtar da shi.
In wani abu daga cikin abinda Allah SW ya aiko Annabinsa da shi ya buya wa mutane, to ko dai su yi adalci ko su zama azzalumai, mai adalcin shi ne wanda zai yi aiki da abinda ya zo masa daga wurin Annabawa ba zai zalunci kowa ba, azzalumi shi ne mai abka wa mutane, wadannan azzaluman sun san cewa zaluncin suke yi, Allah SW yana cewa ((Wadanda aka zo musu da littafi ba su rarraba sai bayan da hujja bayyananniya ta zo musu Al-Bayyina 4)).
Da a ce sun yi aiki da abinda suka sani na adalci da wasu sun sake wa wasu, misalin masu liqe wa malaman fiqihu, sun sani cewa malamannan fa gajiyayyu ne za su iya yin kuskure wurin fahimtar hukuncin Allah SW da manzonsa a wata mas'alar, sai suka maye gurabun Annabi SAW da malaman mazahabobin, suka ce: Abinda za mu iya kenan kawai, mai adalci a cikinsu bai zaluntar kowa, bai abka wa kowa da zagi ko cin mutunci da bakinsa ko a aikace, sai dai ya ce wanda yake binnan shi yake da gaskiya, koda kuwa bai da wata hujja da zai fito da ita, ya kuma abka wa wanda ya saba masa duk da cewa yana buqatar a yi masa hanzari (Fatawa 4/7)".
Ibn Muflih yake cewa: Ibnl Jauziy ya fadi a cikin littafinsa na (As-Sirrul Masun) "Na ga masu jingina kansu da ilimi suna wasu ayyuka kamar na sauran mutane, idan Bahambale ya yi salla a masallacin Shafi'awa bai bayyana Bismilla an ji ba sai Shafi'awan su zuciya, in kuma Bashafi'e ne ya yi salla a masallacin Hambalawa ya bayyana Bismillar sai Hambalawan su zuciya, wannan mas'ala ce da za a iya ijtihadi a cikinta, duk fadan da za a yi a kai son zuciya ne kawai ilimi ya hana".
*GINSHIQI NA TARA*
TARON MUHAWARA
In za ka iya guje wa irin tarurrukan muhawarannan da ake gayyato mutane daga wurare daban-daban to ka yi kawai, wani fa za ka ji har a rediyo ake sanarwa cewa za a tattauna da babban malaminnan na kaza da gawuryaccen dan kaza dinnan a wuri kaza kan mas'ala ta kaza, galibin masu zuwa wurin sun je ne su ga wa za a qure? Zai yi waahala ka ce sun je ne don daukakar addini da shiriyar wane, duk wanda yake goyon bayan wani to nasararsa kawai yake nema, koda bai binciki cewa shi ne a kan daidai ko kuskure ba, ba shakka tauna-tauna ita ce hanya mafi dacewa don isa ga abinda yake daidai cikin abubuwan da aka sami sabani a kai, amma ba irin wanda za a gayyaci mutane su ga yadda za a yi gaja-gaja da wane ba.
Su kansu masu tauna-tauna din in ya kasance ta gayya ce za ka taras mutum kan dage ne kan fahimtarsa ya kuma ba fahimtar kariya ta kowace fuska, ya yi ta tunanin yadda zai abka wa abokin tauna-taunan a maimakon yadda zai gamsar da shi gaskiya ya karbe ta, shi ya sa za ka taras mafi yawan tauna-taunar da ake yi ba wanda yake cewa ya ga gaskiya a maganar dan uwansa ya karba, sai ma ka ga sabanin ya dada fadada, in malamai ne sai ka taras har daliban ya shafe su, in ba malamin ya yi kyakkyawar daukan mataki ba wurin ganin daliban ba su shiga cikin tauna-taunar ba, anan wurin ko a bayan an tashi.
Allah ya jiqan marigayi Gumi, shi nake ganin yadda yake kame bakinsa sau tari bai rama zagin da ake masa na cin mutunci, sai ma cewa yake "Da wanda ya zage ni, da wanda aka zage ni ya ramaman ni dai na yi Allah ya isa" anan bai ba da qofa ga almajiransa su saka baki cikin maganar ba koda kuwa ba ta yi musu dadi ba ko suna da abinda za su fada ko babu, ina son na ce tauna-tauna abu ne mai kyau kuma shi ne ma ya kamata a yi matuqar ana son isa ga gaskiya, amma da sharadin don gaskiyar aka je, kuma qoqarin shiriya ko shiryarwa ake yi, ba shuhura a gaban mutane da sanin lallai wane malami ne kuma qi fadi ba, ina laifi in mutane sun ga wane yana azarbabi a addini a zauna da shi a tattauna matsalar bisa sharadin isa zuwa ga gaskiya "In bayaninka ya bayyana za mu karba, shin in namu ya bayyana za ka karba?".
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa:Abulfawzhaan*