TAMBAYA TA 54


*HUKUNCIN WADDA AKE BINTA AZUMI HAR WANI AZUMIN YAZO TANA SHAYARWA, ZATA CIYAR NE KO ZATA RAMA NE ??*
*Tambaya*

Assalamu alaikum malam inada tanbaya mace ce mai ciki wanda tanada cikin azumin watan ramadan yafara kuma bazata iya azuminba saboda cikin batasamu tarama azuminda tashaba wani azumin yazo. Kuma tana shayarwa. Malam zata iya ciyarwa akan hakan koko saita rama bayan shayarwa?

*Amsa*

Wa'alaykumussalam.
Da farko dai ba daidai bane abar azumi har wani azumin ya zagayo ba'a rama ba indai ba wani dalili karbabbe a shari'a bane ya hana arama, amazhabar malikiyya idan anyi haka bayan an rama sai an ciyar saboda sakaci da akayi...

Yanzu idan zata iya yin azumin to ta rama shi, idan bazata iya ba kuwa sai ta bari sai lokacin da zata iya sai ta rama...

Wasu malamai na fahimtar maganar Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan umar cewa zata ciyar ne saboda hukuncin ta shine hukuncin tsoho /tsohuwa da cewa wannan magana ba itace mafi rinjaye ba.
Don haka dai a rama shi yafi dacewa, wannan itace fatawar malikiyya kuma akanta sheiyhk Bin Bazz ya tafi akai.

Amma idan an dauki waccen magana ta sahabban cen biyu akayi aiki da ita, muna fatar an dace shima insha Allah saboda magana/aikin sahabi hujja ne idan ba wanda ya saba masa kamar yadda yake tabbace a wurin malaman usulu.

Wallahu A'alam.

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

1/06/2020


Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegramπŸ‘‡
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna πŸ‘‡
https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)