WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI
- Kabir Abubakar Asgar

Karanta Tarihi da sanin makamarsa na da muhimmancin gaske. Saboda Tarihin yana taimakawa wajen ganin hoton jiya da fahimtar yau da kuma iya hasashen gobe. Sannan ya kan rage wa mutum damuwa da rudewa a duk sanda ya ga wani sabon abu mai ban takaici ko ban tsoro ko mamaki ko maras dadi.

Hakanan kuma, sakacin da al’umma ke da shi wajen nazartar tarihi da daukan izina daga gare shi na taimakwa wajen qara tsundumawa da al’umma ke yi cikin dimuwa da kurakurai da rashin dacewa da daidai wajen yanke hukunce-hukunce.

A yayin nazarin Tarihi, akwai ababen lura da darussa da dama da masana ke yin tsokaci akan su, tare da nuna muhimmancin sanin makamar su don samun gam-da-katar a cikin nazarin Tarihi da amfanuwa da dimbin fa’idojin da ke cikin Tarihin. 

Daga cikin ire-iren wadannan ababe akwai sanin makamar ta’asubanci da iya mu’amalantar rikicin da ake samu a tskanin sa’anni da kuma halin rashin kara da Tarihi ya shahara da shi da kuma batun alaqar Tarihi da maimai, sai kuma uwa-uba, matsalar gazawar bil adama wajen daukan izina daga Tarihi.
Wannan maqala za ta yi tsokaci taqaitacce akan wasu daga cikin wadannan batutuwa da fatan hakan zai haskaka wa ’yan uwa ko ya tuna musu wasu daga cikin dabarun nazarin Tarihi.

(to be continued)
Post a Comment (0)