Auren Barewa da Mutum
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.
Akwai wata barewa da ta rikiÉ—e da zama mace mai kyawun gaske; son-kowa Æ™in-wanda ya rasa. Wata rana sai ta É—auki akushinta (kwatashi) ta kai shi tsakiyar karofi ta ajiye. Sai ta ce da mutanen da ke wurin, “duk wanda ya É—auki tsakuwa, ya jefa ta daga nan (ta tsaya a daidai wani guri), ta buÉ—e wannan akushi, to shi zai zama mijina”.
Da mutane suka ji haka, sai suka yi ta jefa tsakuwa. Wannan ya jefa bai buÉ—e ba, wancan ya jefa bai buÉ—e, sai can daga Æ™arshe aka samu wani ya yi sa’a ya jefa, akushin ya buÉ—e.
Sai wannan barewa ta ce, “yawwa, yanzu na samu miji”. Saboda haka sai suka rankaya tare da wannan mutum zuwa garinsu dan a É—aura musu aure da wannan mutum. Bayan an É—aura aure, sai ta tare a gidan mijinta.
Duk sanda ranar girkinta ta zagayo, akan tura ta gonad an ciro kuvewar miya. Idan ta je gonar sai ta yi birgima a Æ™asa, ta rikiÉ—e ta koma barewa, ta kira ‘yan’uwanta ta hanyar rera waÆ™a kamar haka:
Cinkalkalkal, cinkalin kalaya
Turmin ‘yankale ya yi furen ceÉ—iya
Tudu na korar tudu da ƙaho
Ban da kwatsa-kwatsa
Ban da ƙanana.
Idan ‘yan’uwanta suka ji haka sai su fito, su zo su taru, su cinye kuÉ“ewar da take gonar. Sai su yi bankwana da ita su koma gida. Ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum, ta É—auki zanenta ta É—aura, ta koma gida tana cewa, “ai dama da gangan aka tura ni ciro kuvewar nan, gashi nan na je ban samo komai ba”.
Da mijin nata ya ga haka, wata rana sai ya bi bayanta bata sani ba. Da isarsa gona sai yaga tana birgima. Bayan ta gama birgima sai ya ga ta koma barewa. Daga nan kuma sai ya ji tana waƙa, bayan gama waƙartata, sai ya ga bareyi sun fito suna cin kuɓewar da take gonar. Shi kuma da ya ga haka sai ya fasa su. A lokacin da yake fasa su, ya ga matar tasa ita ma ta gan shi. Daga nan sai ya dawo gida.
Da barewar nan ta ga abin da ya faru, sai ta yi wuf, ta yi birgima ta koma mutum ta ɗebi kuɓewa ta nufi gidan mijin nata. Da isar ta gida sai mijin ya ce:
Miji: “Wacece wannan?”
Barewa: “ni ce”.
Miji: “ina za ki?”
Barewa: “É—aki”.
Miji: “a’a, koma daji”.
Barewa: “na Æ™i”.
Daga nan sai ya É—auki sanda ya bita da gudu, ya kora ta daji. Tun daga wannan lokaci bata sake koma masa gida ba.
Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.