ADMINS KU JI TSORON ALLAH

*ADMINS KUJI TSORON ALLAH!!! 01*
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 15/ 11/ 1441 wanda yayi dai-dai da 06/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, jama'a wannan dan takaitaccen bayanai ne wanda zanyi akan ADMINS da ma MEMBERS baki daya. Da farko dai idan akace Admins ana nufin Shugaba ko jagora na group, wato wanda ya kirkiri group din shine admin, duk sauran wadanda ake ba admin, tho su kuma sunansu VICE wato mataimaki kenan, domin dolene wanda ya kirkiri group din shine yake da iko ba wani admin. Sannan kuma idan aka ba wani admin tho shima anan ne zai samu damar saka wani ko ba wani admin din. Allah yasa kun fahimta?? Tho idan kun fahimci wannan da kyau zakugane ashe mutum daya shine ainhin Admin a group, duk sauran admins din ana kiransu da vice ne. Ina fatar an fahimta??_

_Tho idan kun fahimta da kyau, ashe yakamata admins su san cewa amana ce members din da suke cikin groups dinsa, kuma dolene wajibi ne Allah zai tambayeshi akan wannan amanar da ya daukowa kansa, ashe kenan idan kun fahimci wannan da kyau yakamata ku dinga kiyaye abubuwan da zaku dingayi acikin group din tunda kune shuwagabanni._

_Bangaren farkon da zanyi magana akai sune wadanda suke bude groups da sunan musulunci, da sunan suna da'awar musulunci, tho yakamata kuji tsoron Allah kuma ku kyautata niyyah kuyi saboda Allah._

_Jama'a wadannan admins din masu bude groups da sunar da'awar musulunci sunada matsala kwarai da gaske, wasu basuda ilimin da zasu iya koyar da kansu balle su koyar da wasu, shiyasa zakuga yanzu groups na addini sunyi yawa barkatai a social media wanda kuma yawancin masu budewa basuda iliminta. Shiyasa zakuga suna dauko rubutun da wasu sukayi su cire lambar masu rubutun, sannan su cire sunar me rubutun su saka nasu. Wallahi haka yawancin masu bude groups da sunan addini suke, bazan ambaci sunan kowa ba, sannan bazan ambaci ire-iren groups da suke haka ba. Amma dai ina mana wasiyya da muji tsoron Allah mu daina cin amanar ilimi, wallahi wannan abinda ake ba dai-dai bane cin amanar ilimi ne, kuma abin mamaki idan akayi musu tambaya a karkashin post din da suka canza zuwa nasu, tho bazasu iya amsata ba, sai dai su damu masu ainhin rubutun da wannan tambayar akan lallai sai an amsa musu. Kuma wallahi yawancin masu irin haka tantirai sunfi yawa acikinsu, wallahi wani kana ganin hotonsa kasan babban tantiri ne baisan komai ba gameda addini, amma saboda rashin kunya sai kaga shima ya bude group da sunan addini saboda yana neman suna, ko kuma yana neman mutane. Akwai lokacin da nayiwa wani daga cikin masu bude groups da sunan addini alhali kuwa basuda iliminta, nace masa inaso mu hadu dashi saboda akwai wata maganan da nakeso muyi, tho sai ya turomin da address dinsa, tho da na samu lokaci naje gidan da yayi min kwantance, tho jama'a ina zuwa gidan sai naga wani mutum baki kirin, na rantse da Allah da naga mutumin na dauka dan pastor ne, saboda yadda naga haskinsa, ya haske wani bangaren ya bar wani bangaren, sannan ya mayar da inda ya bari bai haske ba da yellow, wato ya canza kalar gashinsa zuwa yellow. Tho nayi mishi sallama ya amsa, da ya amsa sai da na tsorata yadda naji muryarsa, sai nace masa Dan Allah ina neman wane me suna kaza da kaza, abinda yacemin shine ko kai mukayi magana da kai zakazo ka sameni. Jama'a kun fahimci wannan maganar nan da kyau?? Wallahi abin sai ya dauremin kai na rasa ma yadda zanyi. Tho bayan mun gama magana da shi sai ya nuna min yaji kuma insha Allah ya daina. Tho ina komawa gida na shiga WhatsApp dina sai naga ya turomin sakon kamar haka:- *Kai baba wallahi wannan maganar taka bazai yiwu ba a yanzu, sai dai nan gaba* wallahi haka ya fadamin, bayan ya nuna min yaji maganar da nayi masa. Saboda haka ashe ba dukkan masu bude groups da sunan addini ne suke da hankali da ilimi ba._

_Sannan admins kuji tsoron Allah kusani cewa zakuyi bayanin duk abinda kukeyi a wayarku, wasu admin din zasu batawa kansu lokaci akan su karantar da jama'a, amma su kuma basa aiki da abinda suke karantar kuma basa zuwa neman karatu. Shiyasa zaka gansu akoda yaushe suna online, hatta a lokacin sallah suna online, tho amma wasu suna barin datarsu a kunne ne suje suyi sallah, amma yawancin masu haka tho basa sallah akan lokaci, sai dai su tsaya bata lokacin su a online. Kuma kafin nayi wannan maganar da nakeyi a yanzu, sai da na zauna da wasun su a kwanakin baya, kuma suka nuna mim cewa zasu daina insha Allah, amma wallahi har yau da nake muku wannan maganar basu daina wannan halin ba._

_Tho jama'a idan kun fahimci wannan bayanan da kyau, zaku gane ashe wasu daga cikin admins suna cin amanar ilimi, sannan suna wasa da ibada, kuma basa aiki da abinda suka karanta Saboda haka kuji tsoron Allah idan kasan kana cikin masu haka._

_Sannan daga cikin dabi'ar da wasu masu da'awa da sunan musulunci suke a group shine bin matan mutane private suna chatting dasu, kwanaki wata ta taba yimin magana akan cewa ya kamata a fadakar da wadannan mutanen masu bude groups da sunan addini da suji tsoron Allah su dinga aiki da abinda suke karantarwa, nace mata meye faru? Tace wani admin ne me suna kaza, kuma sunan group din da ya bude kaza (kamar yadda na fada bazan ambaci suna ba, amma ita ta fadamin sunan mutumin da ya aikata, kuma wallahi nasanshi) tace ya biyota a private yana cemata gaskiya ita kyakkyawa ce, ta hadu ta harhade, saboda haka dan Allah ta turamasa hotunanta zafafa. Ita kuma sai ta tura masa hotunanta da tayi a tsirara, ba complete kaya a jikinta, kuma tace da ta tura mata sai ya dinga yaba mata cewa gaskiya ta hadu, sannan ya kuma tambayarta ta karo wasu. Jama'a tsakani da Allah wannan mutumin ya cancanci ya bude group da sunan addini?_

_Wallahi barnar da wasu admins masu bude group da sunan addini suke ko? Wallahi yafi wasu masu bude group na iskanci, domin shi wanda ya bude group na iskanci, tho dama ya riga ya yarda cewa shi dan iska din ne, tho amma me bude group da sunan addini fah, shi kuma bai yarda dan iska bane shi ba, sai dai shi malami ne ustazu. Kuma babban manufarsu shine don su tara matan mutane, wallahi wasu ma har lambobin mata suke bawa abokanansu. Dan Allah wannan wane irin malami ne wannan?_

_Saboda haka ina kira gareku members da kusan wane irin admin kuke dashi. Shin yanada hali me kyau ko sabanin haka? Na tabbatar zakusani idan har kuna mu'amala dasu. Saboda yawancinku mata kunfi mu'amala da irin wadannan admins din masu da'awa da sunan musulunci, saboda sunfi burgeku, tho kusani ba dukkansu ne masu hankali da ilimi ba, akwai jahilai marasa hankali acikinsu, saboda haka sai kuyi mu'amala dasu yadda zaku fahimci halayyensu._

_Akwai wata baiwar Allah da ta taba fadamin cewa ta taba turawa wani admin me da'awar musulunci hotunanta a tsirara saboda tana sonsa, kuma so take ta gwada shi idan mutumin kirki ne ta fadamasa cewa tana sonshi, tace wallahi da ta tura masa hotunanta a tsirara, sai baiyi mata fada ba, kuma take kara tambaya cewa ya karo wasu. Idan kun fahimci wannan da kyau, ashe yakamata kusan wadanda zaku dinga mu'amala dasu. Idan ba haka ba, sai watarana sun baku fatawar haduwa a hotel, yace miki ai bakomai don ya karanta a hadisi._

_Jama'a ba ina nufin dukkanin masu bude group da sunan addini haka suke ba, a'a yawancin su haka suke, ai ku ma din shaida ne domin kuna ganin abubuwan da suke faruwa, wasunku na kawo min karar irin wadannan mutanen, kuma kuna ganin yadda zaururruka sukayi yawa a social media barkatai, shiyasa zakuga kwata-kwata su basuda tsari. Ina fatar kun fahimta??_

_Sannan akwai wasu bayin Allah wadanda idan suka bude groups, tho aikinsu shine yada karatuttukan malamai aciki, su sanya kudinsu su saye data su dinga yada karatuttukan malamai, kuma basa bada dama ayi magana aciki. Kunga irin wannan tsarin yayi kyau sossai da sossai. Tho amma kuji tsoron Allah kada ku bari wannan aikin ya hanaku yin ibada yadda yakamata ko ya hanaku zuwa neman karatu ko jin Karatun malamai. Ina fatar an fahimta??_

_Zan dakata anan a lekca ta gaba zanyi bayani akan masu bude groups da sunan *hausa novel, soyayyah, ma'aurata,* da dai sauran membobin da suke ciki insha Allah. Allah ta'ala ya datar damu._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Post a Comment (0)