*DAN DUBA MIN WANNAN*
.
Abinda na sani game da daliban ilimi a yau shi ne wannan.
.
لسان الحال
.
أعلمه الرماية كل يوم
. ..... ..... ولما استد ساعده رماني
.
وكم علمته نظم القوافي
. .......... ولما قال قافية هجاني
.
Amma lokacin muna yara in wani ya baci uwayenmu muka sa baki kashi ake ba mu, uwayenmu ba sa yarda mu sanya baki a matsalolin manya, sukan ce in za mu yi to mu yi da tsararrakinmu sam yaro ba zai shiga cikin maganar manya ba.
.
A malamai kuma ina tuna maganganun Mariganyi Gumi lokacin da ake zakinsa, hadewa ya yi yake cewa da wanda ya bace shi, da wanda aka batai ya kare shi shi dai ya yi Allah ya isa.
.
Ban san gaskiyar maganar ba amma tsawon tafiyar sheikh Qala-rawi a Kano da Malam Nasiru Kabara da malam Kabaran ya saki dalibansa tabbas in ba a yi wani abu ba za a yi wani.
.
Qila nan gaba sai malamammu sun sake dawo da tarbiyarmu jasadan da ruhan tukunna kafin mu saitu, ina ganin malamammu sun yarda da hankalin da muke da shi dari bisa dari shi ya sa suka karkata wurin ba mu duk karatun da muke so, suka dan ja da baya kadan da wanda muke buqata a farko.
.
Duk malaman salaf magabata in ka dauko su daya bayan daya lokacin da suke dalibai ka kalli irin ladabin da suka yi wa malamansu, ka kalli yadda suke tsantsani ga shige wa tsararrakin malamansu wadanda suka sami sabani da su, za ka ga mu dalibai a yau yadda muke yi da magabatammu kan wani sabani nasu ba namu ba, sai ka ga akwai bambanci.
.
Ina ganin ba a makara ba in dai za a yi wa tukkan hanci da wuri, lallai muna da buqatar sanin cewa tsuntsun da gashinsa bai fito ba ba ya tashi sama, haka wanda bai iya tsayuwa ba baya tsalle.
.
In dai maganar da ke cewa abinda ka yi wa wani shi za a yi maka to akwai matsala.
______________________
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248