*TAMBAYOYI DA AMSOSHI*
_Shirin *Wasa Kwakwalwa* na Zauren:_
*🕌Irshadul Ummah WhatsApp.*
..
..
*Tambaya ta farko:*
Menene ma'anar *tsarki* a shari'ance?
.
*Amsa:* Tsarki a shari'a shi ne gusar da kazanta (kari) da kawar da najasa.
..
..
*Tambaya ta biyu:*
Ana yin tsarki ne da ruwa tsarkakakke. Ya ruwa mai tsarki yake?
.
*Amsa:* Ruwa mai tsarki shi ne mai tsarkakewa; shi ne ruwan da launinsa, ďanďanonsa da qamshinsa be chanja ba.
..
..
*Tambaya ta uku:*
Waďanne abubuwane suke wajabta wanka?
.
*Amsa:* Abubuwan da suke wajabta wanka su ne: ¹Janaba, ²ďaukewar jinin haila, ³ďaukewar jinin biki (haihuwa).
..
..
*Tambaya ta huďu:*
Menene ma'anar *janaba?*
.
*Amsa:* *Janaba* shi ne fitar maniyyi ta hanyar jin daďi, kamar jima'i, istimna'i, ko wasa tsakanin namiji da mace, ko a cikin barci. Ko kuma shigar al'aurar namiji baligi cikin al'aurar mace.
..
..
*Tambaya ta biyar:*
Wanda ya wayi gari da janaba, be samu ruwan da zai yi wanka ba, ko idan ya ta6a ruwa zai haifar masa da matsala, ga shi yana tsoron fitar lokacin sallah. Ya zai yi kenan?
.
*Amsa:* Zai yi taimama ya je ya yi sallah.
..
..
*Tambaya ta shida:*
Menene *maziyyi?*
.
*Amsa:* Maziyyi farin ruwane tsinkakke da yake fitowa a lokacin qaramar sha'awa, kamar tunani, kallo, rungama d.s. Galibi ya fi fitowa mata fiye da maza, kuma ba a jin lokacin fitarsa sannan kuma ba ya tafiyar da sha'awa.
..
..
*Tambaya ta bakwai:*
Shin maziyyi najasa ne? Menene hukuncin fitarsa?
.
*Amsa:* Eh, maziyyi najasa ne. Hukuncinsa kamar hukuncin fitsari ne, za a wanke al'aura da duk inda ya ta6a.
..
..
*Tambaya ta takwas:*
Shin *maniyyi* najasa ne? Ya matsayin sallar wanda ya yi sallah da maniyyi a tufafinsa?
.
*Amsa:* Maniyyi ba najasa bane a zance mafi inganci, sai dai qazantane da ya kamata a kawar da ita. Wanda ya yi sallah da maniyyi a tufafinsa, sallarsa ta inganta in shaa Allah, sai dai zai fi dacewa a wanke.
..
..
*Tambaya ta Tara:*
Menene ya bambanta wankan janaba, haila da na biki?
.
*Amsa:* NIYYA.
..
..
*Tambaya ta karshe:*
Farillan wanka guda nawane? A lissafo su.
.
*Amsa:* Abin da ya fi inganci shi ne farillan wanka guda biyu (2) ne; ¹Niyya da ²game jiki da ruwa.
..
..
Alhamdulillah. Amsoshin tambayoyin namu kenan na wannan mako. Wanda ďaliban zauren Irshadul Ummah suka amsa. Allah Ya amsa daga gare mu Ya sa shi a mizanin ayyukanmu.
Idan ka ga gyara za ka iya bibiyar admin na zauren Irshadul Ummah don jin kuskuren mu.
Za a iya kasancewa tare da mu a whatsApp ta hanyar turo da cikakken suna da address zuwa wannan number 08166650256.
Ko a telegram 👇
https://t.me/irshadulummah1