*Biology*
*Darasi Na shidda 6*
*TRANSPORT SYSTEM*
Shi transport system yana magana kan zurgazirga (movement) ta bangarori jiki domin samar da abun da jiki yake bukata domin shi kuma jikin yaci gaba daaiki batare da matsala ba.
*need for transport*
To idan har hakan yanada amfani kenan acikin jikin mu to dole yakasance yana da amfani domin rashin sa zaihaifar da matsala. Amfanin nasa sune kamar haka
1.yana rarraba duk wani oxygen da ka shaka acikin jikinka.
2.yana rarraba duk wani nauin sinadarin abinci a dukkan jikinka (nutritional food)
3.yana fitar da duk wani gurbataccen abu wanda yakunshi fitsari dauransu (west product of metabolism)
4.yana fitar da enzyme da kuma hormones wainda suka gama aikinsu (inactive enzymes and hormones) sbd muna da ezymes da hormones da dama wainda ke taimaka mana wanda wani lokaci zasu bayyana ne domin yin aikinsu to dazarar sungama to shikenan Sun gama aiki sai wasu kalar su subayyana.
5.yana rarraba sinadarin ion &mineral acikin jiki
6.yana rarraba zafi domin zafin jiki yadaidaita.
*Materials for transport*
Ainafin kayayyakin da jikin yake transport dinsu
(1) OXYGEN (2) CARBONDIOXIDE (3) NUTRIENTS (4) HORMONES &ENZYMES (5) IONS& MINERALS (6) WATER (7) MANUFACTURED FOOD (8) MINERAL SALT
*COMPOSITION OF BLOOD*
Kamar yadda muka sani shi jini yana da matukar amfani ajiki kana kuma yarabu gida 2
1 Blood cells or capsule. Wanda shi wannan yanayin jinin daskarre ne (solid)
2 Blood plasma. Wanda shikuma wannan blood din yana da ruwa (liquid)
*1 Blood cell or capsule*
Shi wannna sinadarin jinin yarabu gida 3
A)Red blood cell
B)White blood cell
C)blood platelet
A) shi red blood cell ana kiransa red sakamakon sinadarin ions dayamaida sa ja (red) ana kiransa da hemoglobin a turance. kana shi Red blood cell (erythrocytes) yana taimakawa wajen zirgazirgar oxygen daga hunhu zuwa cell din dake a jiki (transfer of oxygen)
B)white blood cells (leukocytes) shi wannan jini baida takamaiman kala (colourless) kana haka sharp dinsa (irregular sharp) kana yana taimakawa wajen bada kariya KO kuma yakar duk wata cuta
C)platelets (thrombocytes)shi yana taimakawa wajen sa jini yai kauri (clotting blood)
*blood plasma*
Shi wannan bangaren jini mai sinadarin ruwa ruwa (liquid)yana dauke da sinadarin ruwa kaso mafi yawa wanda yakai akallah 90%wanda yakunshi aguguwa da dama narkakku aciki wanda yahada da protein,food materials (glucose and amino acid)etc
*functions of blood*
Amfaninsa acikin jiki
1)TRANSPORT(2)IN NUTRITION(3)IN EXCRETION(4)HORMONES(5)PROTECTION(6)REGULATION OF TEMPERATURE(7)CLOTTIN OF BLOOD.
*Muhammad salisu company*
*umyu katsina*