FALALA GUDA GOMA NA GOMAN FARKO NA WATAN ZUL HIJJA


#FALALA GUDA GOMA NA KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZUL-HIJJAH


   Darasi na Farko-(1)

Allah ya daukaka wadan nan kwanaki da falala mai yawa wadanda bai sanya su ba a wani watan da ba shi ba. 

1-Falala ta farko
*"Allah ya yi rantsuwa da wadan nan kwanaki guda goma"* 
Malamai suna cewa; 
"Dukkan abinda Allah yayi rantsuwa da shi,yana nuna mana muhimmanci da matsayin wannan abu ta fuskar daraja da kiyayewa,domin Allah shine mai girma kuma baya rantsuwa da wani abu sai mai girman matsayi da daukaka da falala" Allah yana cewa:
 {ﻭَﺍﻟْﻔَﺠْﺮِ ‏( 1 ‏) ﻭَﻟَﻴَﺎﻝٍ ﻋَﺸْﺮٍ} 
@2 ﺍﻟﻔﺠﺮ. 

●Ibn Kasir yana cewa; 
*ﻭﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﺍﻟﻌﺸﺮ*
 Ana nufin kwanaki goma na farkon watan zul-hijja,kamar yadda Ibn Abbas da Ibn Zubair da Mujaheed da wasu daga cikin magabata"* 
@ﻭﺻﺤﺢ ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ.
 @تفسير ابن ﻛﺜﻴﺮ 

●Imam Dhabary shugaban masu tafsir yana cewa; 
*ﻭﺍﻟﻠﻴﺎﻟﻲ ﺍﻟﻌﺸﺮ* 
*magana mafi daidai awajan malamai shine sune kwanaki goma na farkon watan zul-hijjah,kuma malamai sunyi ijma'i akan hakan"* 
@تفسير ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ


 2-Falala ta Biyu 
*"Sune kwanaki sanannu a wajan Allah wadanda ake aika aiyukan ibada mafi girma acikin kwanakin shekara baki daya*

 Allah yana cewa;
*{ﻭَﻳَﺬْﻛُﺮُﻭﺍ ﺍﺳْﻢَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓِﻲ ﺃَﻳَّﺎﻡٍ ﻣَﻌْﻠُﻮﻣَﺎﺕٍ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﺭَﺯَﻗَﻬُﻢْ ﻣِﻦْ ﺑَﻬِﻴﻤَﺔِ ﺍﻟْﺄَﻧْﻌَﺎﻡِ}* @ﺍﻟﺤﺞ 28:

 Imam Baghawy yana cewa; 
*"Ku ambaci Allah acikin kwanaki sanannu,ana nufin kwanakin goma na farkon watan Zul-hijja,wannan shine fassarar mafi yawan malaman Tafsir,daga cikin su akwai Ibn Abbas da Ibn Umar"*
@تفسير ﺍﻟﺒﻐﻮﻱ 

3-Falala ta Ukku
*"Mafi sune mafi Alkhairi da falalar kwanakin duniya baki daya"* 

Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(mafi alkhairin kwanakin duniya,sune kwanaki goma na farkon watan zul-hijjah)*
 @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ .1133

 Annabi s.a.w yace;
*(Mafi falala da daukakar kwanakin duniya,sune kwanaki goma na farkon watan zul-hijjah,babu kamarsu a wajan Allah.........)* 
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﺑﺮﻗﻢ .1150

 4-Falala ta Hudu 
*"Akwai yinin Arfa acikin wadan nan kwanaki,rana ce mafi albarka acikin yin baki daya,ranace da Allah yake yin gafara ga bayinsa kuma yake alfahari da bayansa awajan Mala'iku kuma itace ranar aikin Hajji mafi girma. 

5-Falala ta Biyar 
*"Acikin kwanakin ne ake yin Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba,wanda Azumi yana kankare zunuban shekara guda biyu"* 

Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)* 
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ .3805 

Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)* 
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ .6335 

Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)* 
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ .3853


           Allah ne mafi sani.


mu haɗu a Darasi na biyu insha Allah
Post a Comment (0)