*HIKIMAR RUBUTA BASHI ?*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum Malam Menene dalilan da suka sanya Sharia ta yi umarni da rubuta bashi?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya shiryar da mutane zuwa kowanne alkairi, daga cikin hakan akwai umarni da abin da zai hana samun sabani tsakaninsu, kamar rubuta bashi da kuma sa shaidu yayin cinikayya, ga wasu daga cikin hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni da rubuta bashi :
*1.* Yanke husuma da sabani tsakanin mutane, saboda in mutum maha'inci ne, zai iya yin jayayya akan bashin da ya ci.
*2.* Kiyaye hakkokin mutane daga barin tozarta, saboda rubutu na daga cikin lamuran da suke kiyaye abubuwa.
*3.* Tsayar da adalci a tsakanin mutane.
*4.* Hana azzalumai yin zalunci.
*5.* Kubutar da abokan mu'amala daga dukkan zargi.
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
9/5/2018
*ZAUREN📚DARUL-ISLAM📚*