GIRMAN MAZAUNAI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_DOMIN SAMUN GIRMAN MAZAUNI ( HIPS) DA GIRMAN DUKIYAR FULANI_*

Macen da take son Mazaunanta suyi manya manya kamar an hura su, ko kuma take son taga nonuwanta sunyi manya-manya kuma ba za su zube ba, sai ta samu kayan Zaki na gona suna da matukar amfanin a jikin mace, ki daure ki dinga yawan shan su, gasu kamar hakà:
* Madara
* Sukari
* Lemo
* Ayaba
* Gwanda
* Kankana
* Abarba
*Bayani:* yar'uwa ki sami kankana ki yankata sai ki sami bulanda mai kyau ki murjeta kamar an markada, itama abarbar kiyi mata haka, ki cire bakin idonta. gwandar ki markade ayar kuma ki dameta kamar fura, lemon kuma kiyi masa sala-sala, sannan a sa bulanda matse shi, bayan kin gama matse su, sai ki tace su ki saka sukari, da madara, sai ki dama, sai ki sa a firji ko ki daure a Leda ki sami kankara ki Dora a Kai idan Yayi sanyi sai ko sha wannan hadin shi ake cewa 
(TATACCIYAR NI’IMA)



Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)