GIZO DA ƁAURE

Gizo da Ɓaure
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari an yi wani attajirin sarki, yana da wata babbar gonar ɓaure. Wata rana wannan sarki yana zaune a fadarsa tare da fadawa ana fadanci, sai ya ce da su, “Ina so a samo min wani mutumin da zai tsinken mini ɓaurena kuma ba tare da ya sha ko ɗaya ba. Idan ya gama zan aurar masa da ‘yata tare da gara mai yawa a matsayin ladan aikinsa”. Da fadawa suka ji haka sai suka saka sanƙira (magawata) ya yi shela (yekuwa) a gari cewa sarki yana neman jama’ar gari a fada.

Da magawata ya yi shela jama'ar gari suka ji sai dukkansu suka taru a fada, da Gizo ya hango wannan taron mutane sai shima ya je ya samu guri ya zauna. Bayan jama’a sun taru sai sarki ya sanar da su dalilin wannan taro. Da kowa ya ji wannan buƙata ta sarki sai aka yi shiru kowa ya kasa magana. Can sai Gizo ya ce da sarki shi zai iya.

Daga nan sai sarki ya sallami jama’a, ya kuma saka fadawa suka raka Gizo zuwa gonar ɓaure. Gizo ya je ya taras da ɓaure ya nuna likif yana ƙanshi. Gizo ya hau tsinkar ɓaure kuma yana sha. Dama yana da tsinken sakatar haƙori da kuma madubi a jakarsa. Idan ya yi aiki sai ya dakata ya sha ɓauren nan sannan ya fito da madubi ya sakace haƙori ya kurkure bakinsa. Idan jama’a suka zo wucewa sai Gizo ya tsiri tofadda yau (yawu ko miyau). Haka Gizo ya yi ta aiki, ashe bai sani ba wata kurciya tana kallonsa.

Da Gizo ya gama aiki sai ya je ya sanar da sarki cewa ya gama. Sarki ya sake haɗa Gizo da dogarawa su kuma ya basu buhuna su je su ɗebo ɓaure. Da suka je gona suna ɗura ɓaure a buhu shi kuma Gizo yana ta tsirtar da yau (yawu ko miyau). Da dogarawa suka ga Gizo yana ta tsirtar da yau sai suka tambaye shi Gizo me yasa ka ke ta tsirtar da yau? Sai ya amsa da cewa ai warin ɓauren nan ne baya so.

Da dogarawa suka koma ga sarki sai suka gaya masa cewa lallai Gizo ya yi aiki mai kyau kuma bai ci ɓauren nan ba, saboda sun ga cewa a lokacin da suke ɗura ɓauren a buhu shi Gizo warin ma damunsa yake yi.

Daga nan sai sarki ya ce da Gizo ya je ya gyara gida. Bayan ya gyara gida aka ɗaura musu aure da ‘yar sarki. Aka haɗa masa goma-ta-arziƙi a gararsa. Aka haɗa amarya da tsofaffi ‘yan ɗaukar gara suka kama hanyar tafiya gidan Gizo.

Bayan sun kai amarya gidan Gizo sun ɗan zauna suna hutawa kafin su watse, sai kurciyar nan ta zo ta hau kan danga tana waƙa tana cewa:

Kai Gizo, kai Gizo,
A can ka ci ɓaurenka,
Har ka kurkure bakinka,
Har ka manto jallonka.

Kurciyar nan ta yi ta maimaita wannan waƙar har sai da matan nan suka ji. Da suka ji sai suka ce kai kutsaya ku ji waƙar da kurciyar can take yi. Da Gizo ya ji haka sai ya ce kai kurabu da ita shirmenta take yi. Sai mata suka ce wane irin a rabu da ita kuma, sai suka yi shiru suka ji abin da kurciya take faɗa tsaf! Da suka ji sai suka ce da Gizo, dama ka ci ɓauren ka yi ƙarya ka ce baka ci ba. Daga nan sai suka kwashe gararsu da amaryarsu suka koma da ita gida.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

 

Post a Comment (0)