GIZO DA ƘOƘI DA KANTU


Gizo da Ƙoƙi da Kantu
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana ce dai, wata rana ce dai, da Gizo da Ƙoƙi da Kantu, suka shirya suka tafi daji farauta. A kan hanyar su ta tafiya, sai suka ci karo da ruwa. Da suka shiga ruwan nan don su tsallake shi, sai Kantu ya fara marmashewa, sai Gizo ya ce da shi, kai Kantu, idan ka ci gaba da marmashewa zan cinye ka. Shi ke nan, sai Kantu ya daure, suka ci gaba da tafiya. Can sun shiga tsakiyar ruwa, sai Kantu ya sake marmashewa, sai Gizo ya juyo ya cinye shi.

Bayan Gizo da Ƙoƙi sun tsallake ruwa, sai Gizo ya ɗaura lilo a gindin wata bishiya yana ta fillawa/hillawa. Can yana cikin lilo yana jin daɗi, sai ya hango wani damo, sai ya bi shi da gudu ya kama damon nan, ya yanka, ya gasa, ya hana ƙoƙi ko hanji.

Da Gizo ya koma ya hau lilonsa yana ta hillo, can sai ya ji cikinsa ya fara ƙugi, sai ya ce da Ƙoƙi cikinsa yana ciwo. Saboda haka sai Ƙoƙi ta goya shi dan ta kai shi gurin mai magani.

Ƙoƙi tana cikin tafiya sai ta zo gindin wata babbar bishiya, tana zuwa gindin wannan bishiya sai ta ji wata tsuntsuwa tana cewa:

Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Shike nan sai Ƙoƙi ta ci gaba da tafiyarta. Tana nan tana ta tafiya, sai ta sake isowa gidin wata bishiyar, sai ta sake jin muryar tsuntsuwar nan tana cewa:

 Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Da Ƙoƙi ta ji haka sai ta ce da Gizo, kana dai ji an ce ba za ka rayu ba ko? Gizo ya yi shiru ya kasa cewa komai. Ƙoƙi kuma ta ci gaba da tafiya. Tana cikin tafiya ta sake isa gindin wata bishiyar, sai ta sake jin muryar tsuntsuwar nan tana cewa:

Tsuntsuwa: Ke Ƙoƙi ina za ki?
Ƙoƙi: Za ni gurin maganar nan.
Tsuntsuwa: In kin je ki ce Gizo ya ci damo ba zai yi rai ba.

Ai kuwa kafin tsuntsuwar nan ta gama rufe bakinta Gizo ya tsuge da zawo. Da Ƙoƙi ta ga haka, sai ta sauke shi daga bayanta, ta zuba masa ido tana kallon abin mamaki. Ba jimawa sai damo ya ce da Gizo, “ta ina zan fito?” Sai gizo ya ce da shi, “fito ta hammata”. Sai damo ya ce, “in fito ta hammata warin hammata ya dame ni. Ta ina zan fito?” Sai Gizo ya ce, “fito ta ciki”. Sai damo ya ce, “in fito ta ciki hanji ya tare ni. Ta in azan fito?” Sai Gizo ya ce, “fito ta, taka shi”. Sai damo ya ce, “in je kashi ya taɓa ni. Ta in azan fito?” Sai Gizo ya ce fito ta hammata. Shike nan sai damo ya fito ta hammatar Gizo. Yana fitowa sai Gizo ya mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.
Post a Comment (0)