"Na'ura Mai Kwakwalwa"
Kashi Na Uku
"GUI = (General User Interface).
Daga Salisu Abdulrazak Saheel
" GUI wato General User Interface
A takaice shine abin da yake baiwa Programmer damar karbar bayanai daga mutanen da suke amfani da manhajar shi, kamar yanzu da muke amfani da Facebook to duk wani bayani da muke tattaunawa koma dai menene to "GUI" yana kaiwa Zukerberg wanda ya kirkiri Facebook din bayanan, bari na baku wani misali: idan zamu hada manhajar Scanning din ciwon ido dolene muna bukatar "I/O" wato (Inputs & outputs) to kunga a bangaren "Input" muna bukatar wani bangaren da zai dauki photon idon wannan mutumin ko kuma ace an dauki photon zamu samu wani waje da za iya saka photon ta wajen kaga wannan zabin yake baiwa likita damar saka photon ido ko kuma daukar photon kai tsaye wannan shine "INPUT" din mu..😀
tunda mun shigar da bayanai sauran ita manhajar (Software) ta sarrafa bayanan sannan ta fitar da sakamako wannan Result din shine "OUTPUT" kunga kenan mun hada I/O Interface..😀
A takaice dai "I/O" sune suke hadewa su bada "GUI"
Zamu iya daukar "GUI" kamar "Apps" amma dai "Module" ne wanda wasu mutane suka kirkira domin sauqaqa mana aiki wajen karbar bayani daga "Users" (masu aiki da wannar software din)
a cikin su akwai:
1. Tkinter
2. wxPython
3. JPython
Da sauransu..
Amma dai wadannan guda "3" sune mafi shahara musamman "Tkinter" mutane sunfi aiki dashi
"Tkinter" yanada Input guda: "19" wadanda sune kamar haka:
1. Button
2. Canvas
3. Checkbutton
4. Entry
5. Frame
6. Label
7. Listbox
8. Menubutton
9. Menu
10. Message
11. Radiobutton
12. Scale
13. Scrollbar
14. Text
15. Toplevel
16. Spinbox
17. PanedWindow
18. LabelFrame
19. tkMessageBox
Idan kukayi la'akari da wadannan "Interface" din ina tunanin zasu taimaka maku wajen hada kowanne kalan manhaja kake so cikin sauki sbd babu wanda ba zaku iya sarrafawa ba a cikin su..
Whatssp Only: 08137350232
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677