SHARHIN FIM ƊIN MARY KOM


SHARHIN FIM ƊIN MARY KOM 

Mary Kom fim ɗin Indiya ne da aka fitar da shi a shekara ta 2014 cikin harshen Hindi. Gaba ɗaya shirin an yi shi ne akan wasan dambe wato boxing. 

Fim ɗin ya samu bada umurni ne daga Omung Kumar, yayin da kamfanonin Viacom18 Motion Pictures da Sanjay Leela Bhansali suka ɗauki nauyin shiryawa. A cikin wannan fim, an nuno jaruma Priyanka Chopra a matsayin wata shahararriyar 'yar wasan dambe ce ta ƙasar india, yayin da jarumi Darshan Kumar da Sunil Thapa suka take mata baya a matsayin miji da kuma mai horaswa. Shirin har wa yau ya bada labarin tasowar 'yar wasan dambe wato Mary Kom Kom har zuwa gagarumar nasarar da ta samu a shekarar ta 2008 a yayin gudanar da wasan dambe na World Boxing Championships a Ningbo. Bugu da ƙari, a wannan fim ne jaruma Priyanka Chopra ta fara rera waƙa inda ta rera wata sassanyar waƙa mai sun "Chaoro". 

Wanda ya fara ƙirƙiro labarin Mary Kom shi ne Saiwyn Quadras, inda ya bada shawara wa Kumar kan cewa ba kowa ne ya san Mary Kom a ƙasar India ba, duk kuwa da irin manyan nasarorin da ta samu. Daga nan sai Kumar ya ziyarci Mary Kom domin neman izinin ta akan yin fim da ya shafi tarihin rayuwarta kafin ta samu lambar yabo ta tagulla a gasar wasanni na 2012 Summer Olympics.

Priyanka Chopra ta samu horaswa ta musamman har na tsawon watanni huɗu kafin ta fara ɗaukar wannan fim, hakan ya taimaka mata wajen samun murɗewar jiki tare da ƙwarewa akan wasan dambe da kuma salon dambe irin na Mary Kom. An fara ɗaukar wannan shiri ne a watan Yuni 2013 a Filmistan, inda a nan ne aka ɗauki sashen dambace-dambace na wannan fim.  

An fara haska wannan fim ne a cikin shekara ta 2014 a bikin Toronto International Film Festival, wanda hakan ya sa ya zama fim ɗin ƙasar India na farko da aka fara haskawa a yayin gudanar da wannan biki. Kuɗin dai da aka kashe wa wannan fim shi ne ₹180 million. 

An fitar da fim ɗin Mary Kom ne a ranar 5 ga watan Satumbar 2014 inda ya samu yabo daga masu kallo har zuwa masu sharhi, musamman ma irin ƙoƙarin da ita jaruma Priyanka Chopra ta yi na hawa wannan matsayi na Mary Kom. A lokacin da fim ɗin ya fita, sai da ya zama fim mafi soyuwa da samun kasuwanci mafi kyau a cikin duk wasu fina-finai da mata suka jagoranta a ƙasar Indiya. Hakan ya ba shi damar kawo kuɗi kimanin ₹1.04 billion a tuƙullumar kasuwancin fina-finan India. Har yanzu dai wannan fim yana daga cikin manyan fina-finan da mata suka jagoranta. 


Fim ɗin Mary Kom ya samu lambobin yabo da dama, cikin su kuwa har da National Film Award wa Best Popular Film Providing Wholesome Entertainment Sannan ya shiga gurbin Filmfare Award wa Best Film da kuma Best Actress wa Priyanka Chopra. Haka kuma Chopra ta lashe gasar Screen Award tare da Producers Guild Film Award Best Actress in a Leading Role da wannan fim.

Kaɗan daga labarin fim ɗin. 

Ƙaramar yarinya Mangte Chungeijang Kom, 'ya ce a wajen wani manomin shinkafa da ke zaune a Imphal,
Manipur. Wata rana sai wannan yarinya ta tsinci wata safar hannu irin ta 'yan dambe a cikin wani tsohon jirgi da ya faɗo a shekara ta 1991 a garin Kangathei. Wannan safa ta ƙayatar da Kom sosai, hakan ya sa ta taso tana mai sha'awar wasan dambe, duk kuwa da cewa mahaifinta ba ya so. 

 Wata rana suna irin faɗan yaran nan, sai ta bi wani yaro da gudu inda a ƙarshe ta tsinci kanta a ɗakin motsa jikin 'yan dambe. Bayan ta gano cewa mai horas da 'yan damben shi ne Narjit Singh, da kuma kocin ƙungiyar dambe na yankin Asiya wato Dingko Singh, Kom sai ta bayyana mishi burinta na son wasan dambe. 

A nan ne ya faɗa mata cewa sai ta zo ɗakin motsa jikin sau talatin kafin ya ɗauke ta, domin ba ya so ya ɗauke ta don tana so kawai face sai ta cancanta. Ai kuwa tana zuwa gida sai ta sanar da mahaifiyarta amma ban da babanta. Daga nan ta fara zuwa. Bayan ta yi kwanaki tana zuwa kocin bai kula ta ba, sai shi Sing ya fara horas da ita saboda naci da taurin kanta. Daga baya sai ya bata shawarar ta canja sunanta zuwa Mary Kom. 

Wata rana sai Kom ta shiga wata ƙaramar fafatawa domin samun kuɗin dawo da saniyarsu da ya zama wajibi iyayenta su siyar saboda talauci. A nan ne ta haɗu da ɗan wasan ƙwallon kafa Onler Kom. Bayan ta lashe gasar zakarun jaha, sai mahaifinta ya tuhume ta kan dalilin da yasa ta ɓoye masa shigarta wasan damben. A ƙarshe ma dai sai ya bata zaɓi kan ko shi ko wasan ta zaɓi ɗaya, hakan ba don ranta ya so ba ta zaɓi wasan. Amma bayan ya kalli wasanta na 2002 Women's World Amateur Boxing Championships ya ga irin nasarar da ta samu sai suka shirya. Kuma ya bata haƙuri bisa rashin fahimtarta da ya yi da fari. Ana haka kuma sai Onler ya nemi aurenta tare da yi mata alƙawarin ba zai taɓa cewa ta bar wasan dambe ba. Bayan ta lashe gasar wasannin 2006 Women's World Amateur Boxing Championships, sai ta amince ta aure shi, duk kuwa da cewa kocinta bai so hakan ba. Bayan aure da ɗan wani lokaci kuwa sai ta samu ciki, hakan ya sa ta bar wasan domin kulawa iyalanta. 

Cikin sa'a kuwa sai Kom ta haifi tagwaye, don haka sai ta fara neman aikin gwamnati. Amma sai ta ƙi yarda ta yi aikin Ɗan sanda saboda tana ganin ta cancanci abinda ya fi hakan. Abin da ya fi harzuƙata ma shi ne, mutane sam sun manta da Ita. Onler sai ya bata shawarar ta koma harkar dambe. Ai kuwa sai ta koma ɗakin motsa jini ta bar mijinta da kula da yaran. Duk da cewa kocinta na fushi da ita akan aurenta, hakan bai hana ta dawowa harkar wasan dambe ba. Duk da cewa ta yi ƙoƙari fiye da abokiyar karawarta, ta rasa wannan wasa saboda rashin adalcin alƙalan gasa. Hakan yasa ta jefe su da kujera, in da hakan ya jawo aka dakatar da ita daga wasanni. Daga baya sai ta rubuta wasiƙar ban haƙuri, in da suka amsa bayan sun ci mata zarafi. 


Daga nan sai Kom ta shawo kan Narjit Singh kan ya horas da ita, domin a tunainta shi kaɗai ne zai iya fito da abin kirki daga gareta. Bayan ya horas da ita sai ta shiga gasar 2008 AIBA Women's World Boxing Championships kuma ta samu zuwa zagayen ƙarshe. Ana haka ne kuma sai Onler ya bayyana mata rashin lafiyar da ɗaya daga cikin yaranta ke fama da ita kuma za a yi masa aiki. 

A wasan da ya biyo baya, Kom sai ta kasa kare kanta in da har abokiyar karawarta ta yi mata wani wawan naushi. A nan ne ta fara ganin gizon mijinta da yaranta a cikin 'yan kallon wasan. Hakan ya taimaka mata ta samu ƙarfinta ya dawo kuma ta ci gaba da gwabzawa, inda a ƙarshe dai ta yi nasara. 

Yayin da ta zo amsar kyautar da ta lashe, sai ta fahimci cewa aikin da aka yi wa yaronta ya yi kyau don haka zai rayu. 
Kuma a sanadin wannan abu da ya faru ne ta samu laƙabin "Magnificent Mary",

JARUMAN SHIRIN 


• Priyanka Chopra - Mary Kom

• Sunil Thapa - M. Narjit Singh

• Darshan Kumar - Onler Kom

• Robin Das • Mangte Tonpa Kom

• Rajni Basumatary - Mangte Akham Kom

• Lin Laishram - Bem-Bem

Bijou Thaangjam - Naobi

• Zachary Coffin - German boxing coach

• Bandari Raghavendra - Peter Michael

Raghav Tiwari - Mangi

• Shishir Sharma - National team coach

• Shakti Sinha - S. Sharma

• Kenny Basumatary - Jimmy

• Ritika Murthy - journalist

• Raghav Tiwari - Mangi

• Binud Kumbang - Lalboi

• Pabitra Rabha Jalah - Asong

• Ramendra Vasishth - Federation official's assistant

• Rajesh Nigam - Federation official's assistant

• Deepak Kumar Singh - Alberto

• Mridul Satam - Young Mary Kom


WAƘOƘIN SHIRIN 


1. "Ziddi Dil" 
2. "Sukoon Mila" 
3. "Adhure" 
4. "Teri Baari" 
5. "Saudebaazi" 
6. "Salaam India" 
7. "Chaoro (Lori)" 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Post a Comment (0)