STATUS

💦STATUS📱

1●Shin ka na tuna cewa duk abin da ka saka a Status/Story dinka ka na da naka kasafin na lada ko zunubi?? Awanni 24 za su yi, amma suna iya zama maka zunubi mai gudana ko lada mai gudana, ka za6i abin da ka ke son gani cikin littafin ayyukanka.

2●Haram yana nan a matsayinsa na haram ko da a STATUS ne! Kowane status sai ka bude ka kalla, ka kalli tsiraici da sunan status! ka kalli abin da bai halatta gareka ba da hujjan cewa ai status ne kuma su suka saka!! To zunubinsu na nan kai ma na ka yana nan!!!

3●Wasu sun mayar da status gurin tallata kansu da rayuwar da suke ciki, me suka ci, me su ka sha, suturarsu, gidansu, motar da suke hawa, nuna ma duniya irin rayuwa ta alfarma da suke ciki da sauransu ba dare ba rana! lallai kambun baka gaskiya ne idan baka sani ba!!!

4●Wasu kuma sun mayar da status gurin bayyana damuwoyinsu, koke koke da korafe korafe, habaice habaice da yada magana, bakanta ma juna ko kokarin bakanta ma wani ko sanyashi cikin damuwa! shin wannan ita ce kadai hanyar magance matsaloli a gurinka? wannan ai kauyanci ne da wauta!!!

5●Kai ne saka izgilanci ga Addinin Allah da musulmai da sunan ai comedy/barkwanci ne a status, hotunan tsaraici da video na nuna tsaraici da barna! Ka sani status din ka kodai kyakkyawa ne ya jawo maka lada, kodai mummuna ya jawo maka zunubi, Sai ka zabi wanda ka ga ya fi maka.

6●Shin abin da za ka saka a Status dinka ABU NE DA ALLAH YA YARDA DASHI? SHIN AKWAI WATA FA'IDA A SAKAWAN? Wani a nan status dinka zai dauka ya a jiye a wayarsa ko kuma ya cigaba da yadawa mai kyau ne ko marar kyau! Ka sani za ka dauki zunubinka da zunubin adadin da suka kalla ko suka yada!

7●Wani ba ya kishin ya daura iyalinsa a status ta ca6a ado, abokanshi su gani kowa ma ya gani! ba ya jin komai bare yayi kishinta! ita ma bakauyar yin hakan shi ta dauka matsayin soyayya! To ga sakon Manzon Allah(SAW) gareka: Allah ba zai yi dubi ga marar kishin iyalinsa ba ranar Alkiyama!!!

Post a Comment (0)