📌 *SALAFUS SALEH 002//*
*Al-Imamu Hasanul Basary* (Allah yayi masa rahama) yace:
_"Ya kai É—an Adam ka sayar da Duniyar ka wajen neman Lahirar ka, sai ka rabauta da su gaba daya, kada ka sayar da Lahirar ka Saboda duniyar ka, sai kayi asarar Duniyar da Lahirar ka gaba daya"._
Wannan Fa'ida tazo a cikin waÉ—an nan littattafai:
```• "Tahzeebul Kamaal" ta Al-Imamul Mizziy (6/116)
• "Hilyatul Auliya" ta Abi Nu'aim (2/143)```
A takaice wannan Fa'ida ta kunshi abubuwa kamar haka:
1- Ana samun Lahira ne ta hanyar fifita ta a kan Duniya da bayar da abin Duniya dan samu Lahira.
2- A duniya ake samun Lahira kuma ake yin tanadin don samun Lahira, kuma a duniya ne Mutum yake bata Lahirar sa yayi asarar Lahirar, idan ya fifita Duniya akan Lahira.
3- Wa'azin magabata bashi da tsayi amma ya kunshi Ilimi da Hikima mai tarin yawa.
4- Ana samun rabon Duniya da Lahira ne gaba daya ta hanyar fifita Lahira akan Duniya, kuma ana asarar Lahira ne tare da Duniya idan an fifita Duniya akan Lahira.
✍ *ANNASIHA TV*
(https://t.me/annasihatvchannel)