TAMBAYA TA 48


*Tambaya:*


Asalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh
Ina maka fatan alkairi. 
Tambaye shine
Ya hallata mace ta bukaci sadakinta yazama Quran (Al- Quran) ya kuma tallafa (ta ha ya sata a islamiya) mata har tayi haddan alkuranir?
.

*Amsa:*


waalaiku mussalam
 
Shi sadaki a musulunci ba dole sai ya zama kudi ba, zai iya zama aiki ko wata kadara ta halas, misali banda irinsu alade ko giya etc. sadakin mace ya halatta ya zama duk wata dawainiyar da za a yi mata wanda sharia ta halatta. Dubi annabi Musa sadakinsa kiwon shekara goma, suratu qasas 27 , kuma Hadithi ya tabbatar da sadakin Rumaisa'u shi ne Kalimatus shahada, ga Hadisin Sahal da ke cikin Bukhari (5121), ko ba shi zai karantar da ita ba ze biya ne ya halatta.

 Duba 
*المغنى كتاب النكاح.*

والله اعلم.

*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
(Abu Ammar). 

*🕌Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah
Post a Comment (0)