*ZAN IYA YIN KITSO A KWANAKI GOMAN ZUL-HIJJA?*
Tambaya
Assalam alaikum, malam don Allah Mace wacce zatayi layya zata iya kitso da tace kai. A wannan kwanakin?
Amsa
Wa alaikumus salam, Annabi ï·º ya hana wanda zai yi layya ya cire wani abu daga gashin sa, kamar yadda ya tabbata a hadisin Ummu - salma.
Zai yi wuya ayi kitso wani gashi bai fadi ba, hakan sai ya nuna barin kitson a wannan kwanakin ga wacce za ta yi layya shi ne daidai.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
5/9/2016
7/Zul-hijja 1437
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
______________________
Ku kasance damu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
👇