ME KA SANI GAME DA SHAIƊAN?
✍ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
29 ga Shawwal 1441H (10/06/2020)
Sheɗan suna ne ko siffa da ake kiran Iblis da shi, wanda Asalin sa daga wuta aka halicce shi, daga jinsin aljanu, an kira da suna iblis a gurarai goma sha ɗaya a cikin Alkur'ani mai girma, kuma halitta na farko daga cikin aljanu wanda ya fara bijrewa umarnin Allah ta'ala, na ƙin yin sujjada ga Annabi Adam AS.
Kuma ana amfani da wannan suna ko siffa akan dukkan aljani ko mutum, wanda ya kangare ya yi tawaye ko ya zama cikin miyagu, har dabbobi idan suka ɗauki wata siffa mara kyau a na kiransu Sheɗanu, kamar yadda Annabi saw ya kira baƙin kare da sheɗan.
Sheɗani shine babban abokin gabar musulmi mumini, bashi da wani aiki dare da rana sai ƙoƙarin halakar da shi da taɓar da shi, da nuna mummunan abu a cikin sura mai kyau da nuna kyakkyawan abu a cikin sura mummuna, D sa masa kasala wajan yin aiki mai kyau, da kuma sa masa nisaɗi a wajan aikata mummuna, domin ya raba shi da imaninsa ko ya rage masa shi ta hanyar saɓo, da duk hanyar da ya sami dama ko ƙarama ko babba.
GURARAN DA AKA AMBACI KAMAR SHEƊAN A CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA
Lafazi ko kalmar sheɗan ta zo a cikin al’kur’ani mai girma sau 88, a cikin surori 36, na Macca 53, na Madina 36., wato anbaton sheɗan yazo da yawa a surorin Macca, saboda lokacin shirka ne da Jahiliyya,.
Sheɗan yana da zuriya da ƙabila da waliyyai da ƙungiya da mabiya da masoya, da mataimaka daga cikin aljanu da mutane, waɗanda suke yaɗa Sheɗanci da fasadi da lalata, da sheganta iri-iri. Kuma shine zai ɗebi kaso mafi yawa daga cikin mutane kusan duk mutum dubu yana da mabiya ɗari tara da casa'in da tara, saboda yadda mutane suke son harkar Sheɗanci.
MAKIRCIN SHEƊAN
Alkur'ani mai girma ya bayyana mana waye sheɗan da siffofin sa da Aiyukan sa, da makircin sa, da tsananin gabar sa da musulmi ko mutum ko aljan, domin ya ga ya raba shi da hanyar tsira, kuma zai fitowa mutum ta duk hanyar da ya ga za ta fiye masa sauƙi, zai iya raba mutum da tauhidi ya koma yana shirka, zai iya raba mutum da sunna ya koma yana bidi'a, zai iya raba mutum da nagarta ya koma yana zina ko luwaɗi ko sha giya, ko ki san kai, zai iya raba mutum da kamewa ya koma yana aikata shashanci da sharholiya bayan da mutum ne mai kamewa, zai iya sakawa mutum tsoro da waswasi ko wata shubuha, ko wata sha'awa ko riya, ko san shugabanci ko mugun son kuɗi ta kowacce hanya, ko ya sawa mutum wani mummunan zato da kokwanto gamai da Allah ko Annabi ko lahira ko Kur'ani, ko ya sawa mutum waswasi akan ibada, yana yi yana sakewa, domin yana cewa ta farko ba ta yi ba.
Sheɗan yana iya halakar da kowa Malamai, Shugabanni, masu kuɗi, Maza mata yara manya, waɗanda ba ya iya halakarwa sune kawai Annabawa, amma duk wanda ba Annabi ba, sheɗan zai iya cusa masa wani abu mara kyau, ko ƙarami ko babba, Annabawa sune kadai ma'asumai (Waɗanda Allah ya tsare, sheɗan baya galaba akan su)
RUBUCE RUBUCEN MALAMAI AKAN SHEƊAN
Malamai sun bibiyi siffofin da halayen sheɗan, da dabaru da yake bi wajan kafawa mutum tarko domin ya halakar da shi daga cikin waɗannan malamai a kwai , Mal Ibn Jauziy ya wallafa littafi mai suna Talbisu Iblis تلبيس ابلس
haka Mal, Ibn Kayyim Aljauziyyah ya wallafa littafi mai suna Igasatul lahafan min masa yidil sheɗan
إغاثة اللهفان من مصايب الشيطان
Waɗannan littafai yana da mahimmanci mu nesu mu karanta su, akwai irin su, wiƙayatul insan min masayidil sheɗan, وقاية الانسان من مصايد الشيطان na Shaikh Wahid, da makamantansu da yawa kamar a cikin Ihyau ulumidden na Al'imam Garzali إحياء علوم الدين.
SIFFOFIN SHEƊAN
1, Girman kai yaki sujjada ga Annabi Adam, bayan kuwa Allah ya sa shi,
2'. Karya ya yiwa Annabi Adam ƙarya cewa wanda ya ci wannan bishiya zai dawwama kuma zai samu mulki da dindindin.
3. Hassada, ya yiwa Annabi Adam hassada na matsayin da Allah ya ba shi.
4. An kira shi ɗagutu saboda komai nasa baya kan tsari.
5. An kira shi maridan wato mai tsarin kai, saboda yaƙi jinin gaskiya.
6. An kira rajem wato jefaffai, saboda babu shi babu rahmarAllah.
7. An kira shi laananne, saboda ya yi nisa daga dukkan alkhairi.
8. An kira shi maƙiyi saboda, mummunar ƙiyayya da yake nunawa duk mai son Allah.
HANYOYIN DA SHEƊAN YAKE BI WAJAN HALAKARWA.
1 Shirka, ko kafirci ko munafinci babba na ƙin Allah da Manzon sa, da ƙin gaskiya.
2 Bidi'a, ƙaramar bidi'a ko babba, ta aikin zuciya ko gaɓɓai, ko ta lafazi,
3 Ragowar manyan saɓo, kamar zina luwaɗi madigo, sata kisan kai, shan giya, caca, fashi , da sauransu, ya kuma hana mutum yin nadama da tuba,
4 Kananan zunubai, domin suna taruwa su zama manya, tunda ana rena su.
5 Shagala da gafala daga abu mai mahimmanci zuwa, mara mahimmanci. Kamar mutum ya shagala da aikin nafila alhalin yana kuma yana sakaci da farilla,
6. Cusawa mutum tsoro da waswasi , da gudun zargi akan gaskiya,
YADDA YAKE SHIGOWA MUTUM CIKIN RAYUWAR SA.
Idan mutum yada da waɗannan siffofi sheɗan yana saurin shiga cikin rayuwar sa ya halaka shi, domin mai waɗannan siffofi, la budda zai zama mabiyin Sheɗani,
1. Jahilcin addini, ba karatu babu tambaya, sai musu da jayayya,
2. Yawan fushi mai tsanani, shi yake kawo saurin ɗaukan mataki, wanda ake da na sani.
3. Tsananin son duniya wanda yake makantar da ido da zuciya. Mutum ya yi ta yin abinda be kamata ba domin kawai ya sami duniya.
4. Tsawaita guri, sai na zama kaza sai nayi Kaza kuma duk akan duniya,
5. Kwaɗayi, wanda zai kai ga zubar da mutunci, da ɓarin lahira akan abin duniya.
6. Rowa, wacce za ta hana fitar da haƙƙin Allah.
7. Girman kai ƙin karɓar gaskiya da walaƙanta mutane,
8. Son zuga kirari da ƙarya da gaskiya,
9. Riya, yin aikin lahira ba don Allah ba don mutane su gani su yaba.
10. Alfahari da taƙama jiji da kai, har yana ganin kowa a banza.
11. Mugun zari da zarmaiwa wajan son abin duniya ga Kwaɗayi ga Rowa.
12. Biyewa son zuciya, mutun yasan gaskiya amma sai ya kauce mata da gangan.
13. Mummuna zato ga Allah ta'ala, da bayin sa.
14. Wulakanta duk wani na ƙasa da kai a komai.
15. Raina zunubi da ɗaukan ba a bakin komai ba, ko kuma a fake da wani aiki, ko wata falala.
16. Rashin sanin Allah gamai da yadda ake samun rahmarsa da yadda ake tsira daga azabar sa, mutum ya zama yana son rahama kuma yana tsoran azaba amma yaƙi bin koyarwar Annabi saw, yana bin wasu hanyoyi daban ba yadda Annabi saw ya bayyana ba.
17. Domin Annabi saw yace: kowa cikin al'umma ta zai shiga aljanna sai wanda ba ya so, sai sahabbai suka ce Ya Rasulallah waye baya so? Sai yace : duk wanda ya yi biyayya a gare ni zai shiga aljanna, wanda kuwa ya ƙi, ba zai shiga ba. Bukhari.
Idan kana son gamuwa da Allah lafiya ka kiyaye abu biyar :
1 Idan Allah ya saka yin abu ka tashi kayi yadda Annabi saw ya koyar.
2 idan Allah ta'ala ya hana abu ka nisanci wannan abun da niyyar biyayya.
3 Idan Allah ya baka kayi godiya da zuci da baki da harshe, kuma kayi amfani da abin wajan yin abinda Allah yake so ya yarda da shi.
4. Idan An jarabceka kayi hakuri, kuma kasan daga Allah ne.
5. Idan ka aikata laifi kayi nadama kayi tuba kayi istigfari, da alƙawarin ba za ka kuma ba.
Allah ka raba mu da sharrin sheɗan, duniya da lahira.