TARBIYYAR 'YA'YA

SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

Tarbiyan Ya'Ya

Tarbiya wata kalma ce da ta samo asali daga Larabci, wacce ke nuni ga reno. Akasari ana amfani da kalmar ce don nuni da yadda muke kula da ‘ya’yanmu.

 Hanyoyin da za’a bi don inganta tarbiya yara.

1. Abu na farko shine cusa wa yaro tsoron Allah. Hanyar cusa wa yaro tsoron Allah kuwa shine shine sanar da shi Allah din da abinda Ya yi umarni da abinda Ya yi hani. A duk lokacin da yaro ya zama mai tsoron Allah da kokarin yin abinda Allah Ya yi umurni, da barin abinda Ya yi hani, tarbiyarsa zai zamo mai sauki a wurin iyayensa, ko yaro na tare da su ko ba ya tare da su.

2. Cusawa yara son ilimi. Kasancewar ilimi shine ginshikin rayuwa, to hakkin iyaye ne su muhimmantar da ilimi wajen tarbiyar ‘ya’yan su. Su yi wannan ta hanyar maida hankali da ilmantar da ‘ya’yan nasu da kuma su kansu iyayen. Ya kamata su dauki ilimi a matsayin haske mai haskaka rayuwa ta ko wani fanni ba wai kawai don neman aikin abin duniya ba.

3. Dole iyaye su kasan ce abin koyi ga ‘ya’yansu. Ma’ana a nan duk wani abinda iyaye za suyi, ya kasan ce irin abinda suke son ‘ya’yansu suyi ne, domin shi yaro yafi koyon abu a aikace fiye da abinda za’a gaya masa. Misali in har uwa bata son yaran ta su koyi zagi da tsinuwa to ta kiyaye zage-zage.

4. Iyaye su kasance masu girmama ‘ya’yan su: A al’adar malam Bahaushe yara a na sa tsammani su kasance masu ji ne da biyayya amma ba su da ikon yin tambaya ko bada shawara. Wannan al’ada ba dai dai bane. Ya dace yaro a karramashi kamar kowa ya zamanto yana da ta cewa a al’amura, sai dai manya su kasance masu kula, da gargadi, da dai-daita al’amura in za'a kauce hanya. Yin haka na baiwa yara daman sanin darajar da suke da shi, da kuma koyon yadda za'ayi hulda da jamma’a in an fita duniya . Girmama yaro yana da ga cikin hanyoyin tarbiya sai mu kula.

5. Yawan kula da abinda yaro ke yi. A matsayin mu na masu kula da ‘ya’yanmu ya zama lallai mu kula da duk wani abinda suke yi. Na san yana da wahala amma wajibi ne in har ana son a yi tarbiya ta kwarai. Kula ba yana nufi hana su sakewa, sai dai yana nufin kasancewa kana/kina sane da inda suke ko abinda suke aikatawa dai dai gwargwadon iyawa a kowani lokaci. Wannan zai ba da ikon sanin halin da yaro ke ciki, sannan in yayi ba daidai ba za a gyara masa.

6. Iyaye su guji yin munanan kalamai a kan yara. Kowa ya sani a addini mugun baki bai da kyau ga ‘ya’ya. Yaro idan ya sosa wa wasu iyayen rai, musamman iyaye mata, sai ka ji ana “Allah wadaran ka wane” ko “ la’a nanne,” da dai sauran munanan kalamai, wanda suna iya binshi, sai ka ga yaro ya shiga yin taurin kai ba zai saurara wa kowa ba, ya zamanto bai da muntunci bai gani wani da mutunci, kuma daga karshe a rasa yadda za’ayi da shi. Allah ya sauwake.

7. Koya wa yaro girmama na gaba da shi. In ka ga yaro na girmama na gaba dashi to ya gani a na yi ne. Iyaye dole su nuna wa ‘ya’yan su muhimmanci girmama babba ko da daga ina mutuminnnan yake, daga kauye ne, birni ne, talakane shi, mai dukiya ne, addinku daya ko ba daya ba. Idan iyaye suka yi haka a aikace to yaro shima zai yi.

8. Koyawa yara kyauta ta hanyar aikatawa. Tarbiya ta kunshi rayuwa ce gurungundumarta, sabo da haka komai ya kamata yana ciki. Kyauta aba ce mai kyau da yara ya kamata su fahimci cewar mutun ya zamanto mai yawan bayarwa ba wai mai yawan tsammaniba. Iyaye su kasance masu kyauta don nuna wa yara mahimmancin kyautar, misali ta hanyar aikensu su kai kyauta gidan dangi ko makota ko dai abokan arziki. Kuma kar a yarda a rika yin gori idan ambayar, sabo da yara suna jin duk abinda iyaye su ke fada, kuma su ma in sun tashi haka za su yi.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)


 Zauren Macen Kwarai

. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.

Post a Comment (0)