TSAFTAR KAI DA MUHALLI


PERSONAL HYGIENE AND ENVIRONMENTAL SANITATION
(Tsaftar Kai da Tsaftar Muhalli)

DAGA ; Abba Haladu Umar
(Hygiene Consultant)

0️⃣0️⃣0️⃣3️⃣

~ CUTUTTUKA MASU YADUWA (INFECTIOUS OR COMMUNICABLE DISEASES)

Ana daukar wadan nan cututtuka ne sakamakon yaduwar kwayar cuta kaitsaye daga mutum zuwa mutum ko sakamakon cizon kwari (insects bite) ko dabbobi da kuma rashin tsafta (lack of hygiene).

Zamu iya koyan yadda zamu kaucewa wadan nan cututtuka ta hanyar
 ~ Tsaftace Iskar mu
 ~ Tsaftace Abuncin mu
 ~ Tsaftace Ruwan mu
 ~ Tsaftace Jikin mu
 ~ Tsaftace Suturar mu
 ~ Tsaftace Gidajen mu
 ~ Tsaftace Kauyukan mu
 ~ Tsaftar Garuruwan mu
 ~ Tsaftar biranan mu
 ~ Hana kwari (insects) zama a muhallin mu.

Sannan muyi amfani da shawarwarin masana kiwon lafiya da kuma amfani da magunguna na riga kafin kwayar cuta kamar MAYA-MAYAN WANKE HANNU masu kashe kwayar cuta.

Tabbas Ayanzu Al'umma na cikin yanayin da tsafta itace mafi muhimman ga rayuwarsu data iyalansu da abokansu da yan uwansu, rashin tsafta yanasa cuta tayadu cikin sauki da hanzari ta kuma yiwa mutane barna mara adadi.

         ISKA (AIR)

Iska itace aba mafi muhimmanci da daraja da jiki ke bukata.

Dan adam zai iya rayuwa na yan kwanaki batare da RUWA ba.

Dan adam zai iya ruyuwa na sati biyu ba batare da ABUNCI ba.

Amma dan adam ba zaitaba iya rayuwa na MINTUNA BIYAR ba batare da ISKA ba.

Iska itace aba ta farko da dan adam ke bukata don ya rayu a duniya.

Shiyasa masana suke cewa abun da yafi komai muhimmanci ga rayuwar dan adam a duk inda yake a duniya kyauta ne watau ISKA.

Sannan fa idan kasamu TEMPORARY CEASE OF BREATHING watau (Dakatawar numfashi na dan wani lokaci) to anan likitoci duk wani taimako da zasu iya baka to acikin mintuna biyar ne kawai.

Duba da muhimmancin da ISKA take dashi ga rayuwar dan adam yana da kyau mu fahimci,
  ~ Ita ISKAR ya take wadanda sinadarai ne suka ginata ?
  ~ Ya ake gane gurbace war ita ISKA ?
  ~ Kuma ya kwayar CUTAR dake yawo acikin ISKAR suke ? 
  ~ Sannan wacce muke irin ISKA muke shaka? 
  ~ Kuma wacce irin ISKA muke futar?
  ~ Wadan da matakai akebi a tsaftace ISKA a muhallin mu?

Ilimi shine jigon cigaban al'umma sanan aiki dashi na karawa al'ummar kwarjini da kima da daraja a idon duniya.

Daga Kungiyar
Arewa Student's Orientation Forum
(ASOF)

Muhadu a rubutu nagaba

✍Abba Haladu Umar
08034343929
Post a Comment (0)