TUNTARWAR MU TA YAU


من كنوز السنة
عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: مَثَلُ مَا بَعَثَنِي اللَّهُ بِهِ مِنَ الْهُدَى وَالْعِلْمِ كَمَثَلِ الْغَيْثِ الْكَثِيرِ أَصَابَ أَرْضًا فَكَانَ مِنْهَا نَقِيَّةٌ قَبِلَتِ الْمَاءَ فَأَنْبَتَتِ الْكَلأَ وَالْعُشْبَ الْكَثِيرَ وَكَانَتْ مِنْهَا أَجَادِبُ أَمْسَكَتِ الْمَاءَ فَنَفَعَ اللَّهُ بِهَا النَّاسَ فَشَرِبُوا وَسَقَوْا وَزَرَعُوا وَأَصَابَتْ مِنْهَا طَائِفَةً أُخْرَى إِنَّمَا هِيَ قِيعَانٌ لاَ تُمْسِكُ مَاءً، وَلاَ تُنْبِتُ كَلأً فَذَلِكَ مَثَلُ مَنْ فَقِهَ فِي دِينِ اللهِ وَنَفَعَهُ مَا بَعَثَنِي اللَّهُ بِهِ فَعَلِمَ وَعَلَّمَ وَمَثَلُ مَنْ لَمْ يَرْفَعْ بِذَلِكَ رَأْسًا وَلَمْ يَقْبَلْ هُدَى اللهِ الَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ. رواه البخاري ومسلم والنسائي وغيرهم

Manzon Allah SAW yana cewa: “misalin abin da Allah ya aiko ni da shi na shiriya da ilmi kamar ruwan sama ne ya sauka a kan kasa, wani bangaren kasar ya kasance lafiyayye, sai ya rike ruwan, sannan ya tsirar da yabanya mai yawa. Shi kuwa dayan bangaren wanda ya kasance faqo ne baya rike ruwa kuma baya tsirar da yabanya. Wannan shine misalin wanda ya fahimci addini kuma ya amfana da abin da Allah ya aiko ni da shi, sannan ya koyi ilmin sunnar kuma ya koyar da shi. Da kuma misalin wanda bai daga kai ya kalli abin da na zo da shi ba bai kuma karbi shiriyar da aka aiko ni da ita ba”.
ALLAH KA SA MU CIKIN MASU BIN SHIRIYAR MANZONKA SAW
Post a Comment (0)