BUDURCI NA 10


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

Fitowa ta daya=*{10}*
*Menene Budurcin nan da ake ta magana akansa?*

_*Budurcin ‘Ya Mace, Ma’anarsa Da Rabe-Rabensa,*_

ALLAH cikin ikon sa da tsari na halitta irin nasa yasa ana haihuwar kowace mace da budurcin ta,

 wannan budurcin shi ake kira da “HYMEN” a turance.
Ita dai Hymen wata fata ce mai dauke da jini a cikinta, 
tana cikin farjin kowace mace amma ba tada wuyar fashewa.

Sannan ba wai Hymen kadai ba ce fatar da ke a cikin farjin mace, a’a. Akwai wasu fatu guda biyu wadanda ake kira a turance da “Labia Minora da Labia Majora”,

 wadannan sune ainahin fatun da ke dauke da farjin mace, amma shi ainahin budurcin yana daga ciki, 

ma’ana, su wadannan “Labia Minora da Labia Majora” sune suke kare budurcin da ke cikin farjin, 
kuma wannan fatar ba mai kwari ba ce sosai, sannan tana yagewa dazarar ta samu takura.

Kalmar budurci ta samo asalinta ne daga kalmar budurwa,
kuma kalmar tana da harshen damo. Budurwa kuwa a Hausance ita ce ‘ya mace wadda ba ta taba yin aure ba, kuma ba ta taba saduwa da namiji ba.

 A littafin Risala cewa aka yi “Budurwa ita ce ‘ya macen da *(cinta, shanta, suturarta, tarbiyarta da hakkin aurar da ita,)*
 suka rataya a kan *Ubanta.*

Kenan, ana iya cewa, budurci wani lokaci ne da ‘ya mace ke shiga na tsakanin balagarta zuwa lokacin da ta yi auren farko.

Wasu malamai sun kara haske da cewa “Lokacin budurci yakan fara daga shekara goma (10)
zuwa sha biyar (15)”.

A wannan lokaci ne za a ga masoya (maza) sun fara kai mata hari da sunan suna son ta. Haka kuma za ta zama abokiyar son kowa; wasannin da ta ke yi da can lokacin kuruciya za ta rage, saboda balaga ta fara shigo ta, ta fara jin kunya; 

saboda wasu abubuwa sun fara bayyana a jikinta, kamar Nono da sauransu.
Kuma a wannan lokaci ne take ji da kanta, tana ganin kanta daidai da kowa,

Muhadu agaba insha Allah,

*GABATARWA Miftahul ilmi*

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)