BUDURCI NA 24


_*======BUDURCI NA=====*_

*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*

*Fitowa ta daya=*{24}

Abin mamaki da takaici ne kaga yarinya mai hankali da tarbiyya agidan su kaga tana Kula irin wadan mazan wadanda burin sulalata rayuwar yarinya subar ta da cizon yatsa kuma kaga har suna alfahari da yin hakan kai kadauka ba mace bace ta haifesu ko ta renesu,

A irin wan nan halin ne zakaga mutum mai mutunci da kima yaga yarin yana sonta da aure Amma saboda bashi da irin wan nan dabi'a sekaga tajuya masa baya wai shi bai waye ba saboda baya kai hannunsa jikin ta tana ganin shi bagidajene ko kuma tace ai shi ustazune ita kuma holewa take da bukata,

Daga nan idan akayi rashin sa'a sheidan yayi nasara akansa shikenan se ya biye mata suyi ta lalatar su awaje suko iyaye Basu saniba,

Wallahi akwai wanda ya min da tambaya wai yanada budurwa kuma sun shaku Sosai har takai ga yayi mata ciki awaje Amma anzubar da cikin toh yan sun tuba kuma ita tace lalle shi takeso ta aura shikuma yana ganin bai kamata ya auri yar iskaba wadda ta bayar da kanta gareshi tun awaje Dan haka shi yanaso ya auri mace tagarine,

Tam bayarsa shine wai yanxu idan yaki aurenta yayi laifi a gurin Allah?
Alokacin naji arainΓ£ inama yana kusa Dani ne ba awaya yake min wan tambayar ba naji kamar innemi inda yake nasa akamashi Amma sena tuna ai yace yatuba kuma tuba yana goge duk wani zunubi da bawa ya Aikata matuqar ba shirka yamutu akaiba,

Amma Dan Allah kujifa shi yalalata mata rayuwa kuma yanzu yanaso yasamu mafaka a shari'a yagudu yabarta ko wayakeso ya aureta?

Niko na ta qar Qare nabashi amsa de de ta tambayar sa dakuma nuna masa irin muni aikin da yayi da cin amanar Allah da manzon sa da iyayen yarinyar da yayan da zata Haifa da danginta da sauran musulmi da musulunci,

*Ya Allah muna rokon ka da ka Kare mana mutuncin Dana iyalenmu da sauran Al'ummar musulmi kasa Mufi karfin sheidan*

_*Allahumma Ameen yΓ£hayyu-yΓ£Qayyum*_
🀲🏼🀲🏼🀲🏼

_*Muhadu agaba insha Allah,*_


_*GABATARWA Miftahul ilmi*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*πŸ‘‡πŸ½
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan NumberπŸ‘‡πŸ½
07036073248
Post a Comment (0)